Zargin Gwamnatin Uganda Da yi Wa Mutane Kisan Gilla.
Kisa Ba Bisa Doka ba A kasar Uganda
Kamfanin Dillancin Labarun Reuters ya ambato ministan harkokin cikin gidan Uganda yana yin watsi da zargin da kungiyoyin kare hakkin bil'adama su ka yi wa gwamnatin kasar na yi wa mutane kisan gilla.
j.j. Odingo ya ce; sojojin kasar sun kare kansu ne daga harin da 'yan tawaye su ka kai,
Kungiyar kare hakkin bil'adama ta "Amnesty International" ta zargi sojojin kasar ta Uganda da kashe mutane ba bisa doka ba a yankunan kabilun kasar.
Kungiyar ta Amnesty ta ci gaba da cewa; sojojin na Uganda su bude wuta akan mutane ba tare da hakan ya zama dole ba, da a karshe ya yi sanadin mutuwar da dama daga cikinsu.
Majiyar gwamnatin Uganda ta ce; An kashe masu gadi 46 da 'yan sanda 16 a wani harin da jami'an tsaro su ka kai a fadar sarkin kabilar Ronzoro, Charlse Wisly mumbire. Tuni dai jami'an tsaro su ka kame sarki bisa zarginsa da kisa.
Har ila yau, kungiyar ta yi kira da a bude bincike akan yadda jami'an tsaron kasar su ke gudanar da aikinsu.