Mar 20, 2019 05:41 UTC
  • Duniya Na Ci Gaba Da Aikewa Da Kayan Agaji Zuwa Kasashen Da Mahaukaciyar Guguwa Ta kada

Kasar Tanzania na daga cikin wadanda su ka aike da kayan agaji zuwa kasashen Mozambique, Zimbabwe da Malawi da mahaukaciyar guguwar Idai ta rutsa da su.

Kayan agajin sun kunshi abinci da kayayyakin kiwon lafiya. Rahotannin sun ce yawan kayan abincin da Tanzania ta aike sun kai ton 214 da kuma ton 24 na magunguwa da kayayyakin kiwon lafiya.

Kasar Afirka Ta Kudu da Asusun kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ( UNICEF) suna cikin na farko-farkon da su ka aike da kayan agajin zuwa Kasashen da bala’in na dabi’a ya shafa.

Ita ma kungiyar Tarayyar Turai ta aike da taimakon kudaden da su ka kai Euro miliyan 3.5 a matsayin taimakon gaggawa zuwa kasashe uku.

Mozambique ta sami euro miliyan 2 daga taimakon na Tarayyar Turai, sai Zimbabwe Euro miliyan 1, yayin da Malawi ta sami rabin miliyan na Euro.

 

Tags