Mar 20, 2019 05:49 UTC
  • Afrika Ta Tsakiya: Masu Dauke Da Makamai Sun Bukaci Firaminista Ya Yi Murabus

A Afrika ta tsakiya, wasu gungun masu dauke da makamai 11 daga cikin 14 da suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, sun bukaci fira ministan kasar, Firmin Ngrebada, da ya yi murabus.

A cikin wata sanarwar da suka fitar wacce kamfanin dinlancin labaren AFP, ya samu, gungun 11 sun bukaci tattaunawa ta kai tsaye da shugaban kasar, inda sukayi watsi da duk wani shirin shiga tsakani na firaministan kasar.

Gungun kungiyoyin sun fitar da wannan sanarwa ce a birnin Adis Ababa, na kasar Habasha, inda ake wani taro karkashin jagorancin kungiyar tarayya Afrika na waiwaye akan yarjejeniyar da aka cimma tsakanin gwamnati da gungun masu dauke da makaman na kasar ta Jamhuriya Afrika ta Tsakiya.

Daga cikin gungun da suka bukaci murabus din firaministan kasar da kuma kafa gwamnatin hadin kasa, harda kungiyar Seleke ta galibi musulmi da kuma kungiyar UPC da kuma MPC.

Gungun masu dauke da makamman sun ce har yanzu suna mutunta yarjejeniyar da aka cimma kwanan baya, amma basu gamsu da yadda gwamnatin kasar ke aiwatar da ita ba.

 

Tags