Kungiyar "Amnesty International" Tana Tuhumar Kenya Da Muzgunawa Yan Hijirar Kasar Somaliya.
An zargi gwamnatin Kenya da muzgunawa yan kasar Somaliya
Kamfanin Dillancin Labarun Associated Press ya ambato kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International tana tuhumar gwamantin kasar Kenya da takurawa yan gudun hijirar kasar Somaliya, da kuma tilasta musu komawa kasarsu.
Kungiyar ta kare hakkin bil'adama ta kuma ci gaba da cewa; Gwamnatin kasar Kenya tana sane da cewa da akwai yiyuwar idan yan gudun hijirar sun koma gida za a kashe su.
A cikin watan August, kungiyar ta Amnesty International ta yi hira da yan Somaliya 65 da su ke a sansanin yan gudun hijira da ke Dadav akan halin da su ke ciki.
A cikin watan Mayu ne dai gwamnatin kasar ta Kenya, ta mayar da 'yan gudun hijirar Somaliya da adadinsu ya kai 280,000.