-
MDD:Sharadin Farfado Da Kasar Sudan Ta Kudu, Zartar Da Yarjejjeniyar Sulhu
Jan 02, 2018 06:27Mataimakiyar Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Kan al'amuran wanzar da zaman lafiya ta sanar a jiya Litinin cewa duk wani shiri na farfado da kasar Sudan ta kudu ba zai yiwo ba har sai an zartar da yarjajjeniyar sulhun da aka cimma a shekarar 2015.
-
Kwamitin Tsaro Ya Sake Sanya Wa Koriya Ta Arewa Takunkumi Saboda Gwajin Makamai Masu Linzami
Dec 23, 2017 05:22Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya sake sanya wa kasar Koriya ta Arewa wani sabon takunkumi sakamakon sake gwajin makamai masu linzami masu cin dogon zango da kasar ta yi.
-
Amurka Ta Hau Kujerar Naki Dangane Da Kudurin Kwamitin Tsaro Kan Birnin Kudus
Dec 19, 2017 05:35Kasar Amurka ta hau kujeran naki dangane da wani kuduri da Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya so fitarwa a daren jiya da nufin kiran gwamnatin Amurka da ta janye matsayar da ta dauka na bayyana birnin Kudus a matsayin babban birnin haramtacciyar kasar Isra'ila.
-
Kwamitin Tsaron MDD Zai Tattauna Kan Matakin Da Trump Ya Dauka A Kan Birnin Qudus
Dec 17, 2017 06:37Kwamitin Tsaron MDD ya fara gudanar da bincike kan koken da kasar Masar ta shigar na watsi da sabon kudirin shugaban kasar Amurka Donald Trump kan birnin Qudus.
-
Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya Ya Gargadi Bangarorin Da Suke Rikici Da Juna A Sudan Ta Kudu
Dec 15, 2017 12:20Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya gargadi bangarorin da suke rikici da juna a kasar Sudan ta Kudu da su nisanci ci gaba da kunna wutan rikici a yankin.
-
Matsayin Qudus : Kwamitin Tsaro Na MDD Ya Juyawa Amurka Baya
Dec 09, 2017 05:54Kwamitin tsaro na MDD ya maida Amurka saniyar ware dangane da matakin shugaba Donald Trump na ayyana Qudus a matsayin babban birnin yahudawan sahayoniya 'yan mamaya na Isra'ila.
-
Kwamitin Tsaro Zai Gudanar Da Zaman Gaggawa Kan Sanarwar Trump Kan Birnin Qudus
Dec 07, 2017 05:53Kwamitin tsaron MDD zai gudanar da wani zama na gaggawa a gobe Juma'a don tattaunawa kan sanarwar da shugaban Amurka Donald Trump yayi na sanar da birnin Qudus a matsayin babban birnin haramtacciyar kasar Isra'ila da kuma shirin mayar da ofishin jakadancin Amurka zuwa birnin na Qudus daga Tel Aviv.
-
MDD Ta Kara Yawan Dakarunta Da 900 A Afrika Ta Tsakiya
Nov 15, 2017 16:56Kwamitin tsaro na MDD, ya amunce da gagarimin rinjaye da karin yawan dakarunsa da 900 da kuma tsawaita aikin tawagar da shekara guda a Jamhuriya Afrika ta Tsakiya.
-
Kasashen Afirka Na Bukatar Kujeru Biyu A Kwamitin Tsaro Na MDD
Nov 12, 2017 05:52Wakilin kasar Aljeriya a MDD Mohammed BESSEDIK ya bukaci a gudanar da canji tare da bawa kasashen Afirka kujeru biyu na din din din a kwatinin tsaro na MDD.
-
Kwamitin Tsaro Ya Bukaci Saudiyya Ta Kawo Karshen Killace Yemen
Nov 09, 2017 05:48Kwamitin tsaro na Majalisar dinkin duniya a bukaci kawacen da Saudiyya ke jagoranta da ya kawo karshen killacewar da ya yi wa kasar Yemen dake fuskantar barazana yunwa irinta mafi muni a shekarun goma da suka gabata.