-
MDD Na Kara Matsin Lamba Ga Gwamnatin Myanmar Kan 'Yan Rohingya
Nov 07, 2017 14:42Kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya kira gwamnatin Myanmar data kawo karshen aikin sojinta a yankin Rakhine da kuma baiwa daruruwan musulmin Rohingya dake gudun hijira a kasar Bangaladash damar komawa gida.
-
Kwamitin Tsaro Na MDD Ya Bukaci A Kare Yara A Lokutan Yaki
Nov 01, 2017 05:41Kwamitin sulhu na MDD ya bukaci dukkan bangarorin dake da hannu a duk wani rikici dasu kare yara a wuraren da ake yake-yake tare da neman kare hakkokinsu a irin wannan yanayi.
-
Rasha Ta Ki Amunce Tsawaita Binciken Makamai Masu Guba A Siriya
Oct 25, 2017 11:20Kasar Rasha ta hau kujerar na ki kan kudirin da Amurka ta gabatar ga kwamitin tsaro na MDD, kan tsawaita binciken da ake kan zargi da amfani da makamai masu guba a Siriya.
-
Kwamitin Tsaro MDD Zai Yi Zama Kan Batun Myammar
Sep 26, 2017 06:43Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai yi wani zama a ranar Alhamis mai zuwa domin tattauna batun kasar Myammar.
-
MDD Ta Bayyana Rashin Amincewarsa Da Zaben Raba Gardama A Yankin Kurdawan Iraqi
Sep 22, 2017 04:46Komitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya bayyana rashin amincewarsa da zaben raba gardawa don bellewar yankin kurdawa na kasar Iraqi daga kasar.
-
Koriya Ta Arewa Na Daf Da Mallakar Makamin Nukiliya
Sep 16, 2017 05:44Shugaba Kim Jong-Un, na Koriya ta Arewa ya ce kasarsa na daf da mallakar makamin nukiliya, wannan kuwa duk da jerin takunkuman da kasashen duniya ke kakaba ma kasar ta sa.
-
Kwamitin Tsaro Na MDD Zai Yi Zama Kan Batun 'Yan Rohingyas
Sep 12, 2017 05:51A wani lokaci, yau Talata ne kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai yi wani zama domin tattauna batun 'yan Rohingyas.
-
MDD Ta Kakabawa Koriya Ta Arewa Sabbin Takunkumai
Sep 12, 2017 05:50Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da gagarimin rinjaye da kudirin Amurka na tsananta wasu jerin sabbin takunkumai kan Koriya Ta Arewa bisa gwajin makamin nukiliyarta na baya baya nan.
-
Amurka Ta Bukaci A Kada Kuri'ar Kakabawa Koriya Ta Arewa Sabbin Takunkumi
Sep 09, 2017 05:44Amurka, a hukumance, ta bukaci a gudanar da zaman Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya don kada kuri'a kan daftarin kudurin da ta gabatar don kakabawa Koriya ta Arewa sabbin takunkumi saboda gwajin makaman nukiliya da ta yi kwanakin baya.
-
Kwamitin Tsaron MDD Ya Bukaci Gwamnatin Burundi Da Ta Kara Ba Wa MDD Hadin Kai
Aug 11, 2017 05:45Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci gwamnatin kasar Burundi da ta ci gaba da ba da hadin kai da kuma aiki tare da kungiyoyin kasa da kasa musamman MDD da sauran kungiyoyin kasa da kasa na yankin.