Sep 26, 2017 06:43 UTC
  • Kwamitin Tsaro MDD Zai Yi Zama Kan Batun Myammar

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai yi wani zama a ranar Alhamis mai zuwa domin tattauna batun kasar Myammar.

A yayin zaman kwamitin zai tattauna batun musulmin Rohingyas da MDD ta bayyana da yunkurin share wata kabila daga doron kasa a kasar ta Myammar.

Babban sakatare na MDD ne Antonio Guterres zai yi jawabi a zaman da kasashe bakwai ciki har da Amurka da Faransa suka bukata.

Shugaba Emanuelle Maccron na Faransa ya danganta batun da kisan kiyashi, a yayin da takwaransa na Turkiyya  Recep Tayyip Erdogan ya danganta lamarin da ta'addancin 'yan addinin Buda.

A halin da ake ciki dai alkalumman da hukumomin Bangaladash suka fitar sun nuna cewa 'yan gudun hijira rohingyas kimanin 800,000 suka tsallaka kasar.

Tags