Rasha Ta Ki Amunce Tsawaita Binciken Makamai Masu Guba A Siriya
(last modified Wed, 25 Oct 2017 11:20:28 GMT )
Oct 25, 2017 11:20 UTC
  • Rasha Ta Ki Amunce Tsawaita Binciken Makamai Masu Guba A Siriya

Kasar Rasha ta hau kujerar na ki kan kudirin da Amurka ta gabatar ga kwamitin tsaro na MDD, kan tsawaita binciken da ake kan zargi da amfani da makamai masu guba a Siriya.

A gobe Alhamis ne ake sa ran kwararun MDD zasu gabatar da rahoto kan binciken na zargin da AMurka take wa gwamnatin Siriya na amfani da makamai masu guba a yankin Khan Cheikhoun a ranar 4 ga watan Afrilu da ya gabata.

Rasha dai ta bukaci da a jira rahoton kwararun kafin a kai ga gabatar da wani kudiri kan gwamnatin ta Damascos.

Ko baya ga Rasha, kasar Bolivia ta nuna adawa da wannan kudirin, a yayin da kasar Sin ko China ta yi rawar kuri'arta.