Koriya Ta Arewa Na Daf Da Mallakar Makamin Nukiliya
(last modified Sat, 16 Sep 2017 05:44:37 GMT )
Sep 16, 2017 05:44 UTC
  • Koriya Ta Arewa Na Daf Da Mallakar Makamin Nukiliya

Shugaba Kim Jong-Un, na Koriya ta Arewa ya ce kasarsa na daf da mallakar makamin nukiliya, wannan kuwa duk da jerin takunkuman da kasashen duniya ke kakaba ma kasar ta sa.

Babbar manufar son cimma wannan shirin na makamin nukiliya, shi ne jerawa da Amurka a fannin karfin soji a cewar shugaba Jong-Un.

Kalaman na Jong-Un na zuwa ne bayan sabon gwajin makami mai linzami da kasarsa ta yi a jiya Juma'a wanda ya ratsa ta sararin samaniyar Japan, abin da ya haifar da sabuwar fargabar tashin hankali a yankin.

Koriya ta Arewa  dai ta yi barazanar nutsar da Japan a karkahsin kasa da kuma mayar da Amurka toka da makaminta na nukiliya saboda goyan bayan sabbin takunkuman da aka kakaba ma ta.

A wani zaman gaggawa da ya yi a jiya Juma'a kwamitin tsaro na MDD ya yi allawadai da sabon gwajin yana mnai cewa abin ya wuce barazana a yankin, hasali ma barazana ce ga duk kasashe mambobinta.