-
Libya: Gargadi Akan Yiyuwar Shigar 'Yan ta'adda Cikin Kasar Libya Daga Waje
May 22, 2017 14:44Gwamnatin Libya ta sanar da cewa da dama daga cikin kwamandojin 'an ta'adda suna shigar kasar ne daga waje.
-
MDD Ta Bukaci Sakin Dukkanin Bakin Haure Da Ake Tsare Da Su A Kasar Libiya
May 22, 2017 01:48Hukumar Kolin Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwarta kan irin mummunan halin da bakin haure da 'yan gudun hijira masu neman mafaka suke ciki a wajajen da ake tsare da su a kasar Libiya.
-
MDD Ta Bukaci Kawo Karshen Tashe-Tashen Hankula A Kasar Libiya
May 21, 2017 07:42Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira ga dukkanin bangarorin da suke fada da juna a Libiya musamman a kudancin kasar da su dauki matakin sulhunta junansu da nufin samun zaman lafiya da sulhu.
-
Libya: Hari A Wani Barikin Soja Ya Kashe Mutane 141
May 20, 2017 01:56A jiya da dare ne kakakin sojan kasar Libya Ahmad al-Mismari ya ce; An kai hari akan sansanin soja a garin Burak wanda ya ci rayukan abinda bai gaza mutane 141 ba.
-
Sojojin Khalifa Haftar Sun Kwace Sansanin Sojin Sama Na Brak Shati Da Ke Kusancin Kasar Libiya
May 19, 2017 07:32Sojojin gwamnatin rikon kwaryar Libiya mai matsuguni a garin Tobruk sun kwace sansanin sojin saman Brak Shati da ke kudancin kasar bayan mummunan gumurzu tsakaninsu da sojojin gwamnatin hadin kan kasa da ke birnin Tripoli fadar mulkin kasar.
-
Jami'an Tsaron Italiya Sun Tseratar Da 'Yan Ci-Rani Fiye Da 2000 Daga Nutsewa
May 19, 2017 01:03Jami'an tsaron kasar Italiya masu gadin iyakokin ruwan kasar sun tseratar da wasu 'yan ci-rani fiye da 2000 da suke hankoron tsallaka wa zuwa cikin kasar ta Italiya ba bisa ka'ida ba,a lokacin da igiyar ruwa take neman kifan da kananan jiragen ruwan da ke dauke da su.
-
Kasar Italiya Zata Kara Taimakawa Libiya A Fagen Yaki Da Fataucin Bakin Haure
May 16, 2017 07:45Gwamnatin Italiya ta gabatar da tallafin jiragen ruwan sintiri guda hudu ga kasar Libiya da nufin shawo kan matsalar fataucin bakin haure zuwa kasashen yammacin Turai ta hanyar teku.
-
'Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Wani Wurin Tsaro A Birnin Tripoli Na Libya
May 14, 2017 07:44Wasu gungun 'yan bindiga sun kaddamar da farmaki a kan wani wurin tsaro da ke karkashin gwamnatin hadin kan kasa a birnin Tripoli na kasar Libya.
-
Libya: An Jefa Dubban 'Yan Gudun Hijira A Gidajen Kurkuku
May 10, 2017 08:24Jami'in da ke fada da hijira da ta sabawa doka a Libya ya ce adadin wadanda ake tsare da su sun kai 7000.
-
Majalisar Dinkin Duniya Ta Bukaci Tallafawa Kasar Libiya A Fagen Siyasa
May 09, 2017 15:01Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Libiya ya bukaci tallafawa kasar ta Libiya domin bunkasa ci gaban siyasar kasar ba tare da daukan matakin tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar ba.