Libya: Hari A Wani Barikin Soja Ya Kashe Mutane 141
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i20536-libya_hari_a_wani_barikin_soja_ya_kashe_mutane_141
A jiya da dare ne kakakin sojan kasar Libya Ahmad al-Mismari ya ce; An kai hari akan sansanin soja a garin Burak wanda ya ci rayukan abinda bai gaza mutane 141 ba.
(last modified 2018-08-22T07:00:08+00:00 )
May 20, 2017 01:56 UTC
  • Libya: Hari A Wani Barikin Soja Ya Kashe Mutane 141

A jiya da dare ne kakakin sojan kasar Libya Ahmad al-Mismari ya ce; An kai hari akan sansanin soja a garin Burak wanda ya ci rayukan abinda bai gaza mutane 141 ba.

A jiya da dare ne kakakin sojan kasar Libya Ahmad al-Mismari ya ce; An kai hari akan sansanin soja a garin Burak wanda ya ci rayukan abinda bai gaza mutane 141 ba.

Ahmad al-mismari ya zargi kungiyar da ta ke dauke da makamai agarin Misarata da kai hari. 

Mafi yawancin sojojin da aka kashe din wadanda su ke a karkashin Halifa Haftar ne da ke iko da yankuna da dama na gabacin kasar.

Harin ya zo ne bayan da aka sami fahimtar juna a tsakanin Halifa Haftar da kuma pira ministan  gwamnatin hadin kan kasa,. Faez al-Siraj.

Libya, tana fama da matsalolin tsaro tun 2011 da aka kifar da gwamnatin Mu'ammar Khaddafi.