MDD Ta Bukaci Kawo Karshen Tashe-Tashen Hankula A Kasar Libiya
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira ga dukkanin bangarorin da suke fada da juna a Libiya musamman a kudancin kasar da su dauki matakin sulhunta junansu da nufin samun zaman lafiya da sulhu.
Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana tsananin bakin cikinsa kan rikicin da ya kunno kai a sansanin sojin Brak Shati da ke kudancin kasar Libiya da ya kai ga lashe rayukan mutane masu yawa, don haka ya jaddada bukatar kawo karshen duk wani rikici da tashe-tashen hankula a kasar.
Babban sakataren na Majalisar Dinkin Duniya ya kuma jaddada cewa: Matakin fada da juna ta hanyar amfani da makamai ba zai taba warware rikici da dambaruwar siyasar Libiya ba, don haka dole ne a kan dukkanin bangarorin da ba su ga maciji da juna, su dare kan kujerar tattaunawa a tsakaninsu da nufin warware duk wani sabanin mahanga.
Tun bayan bullar rikici tsakanin sojojin kasar Libiya kan mallakar sansanin sojin Brak Shati da ke kudancin kasar, mutane fiye da 140 ne suka rasa rayukansu.