-
Masar: Muna Fatan Mohammad Salah Zai Buga Gasar Cin Kofin Duniya Duk Da Raunin Da Ya Samu
May 27, 2018 13:25Ministan wasanni da matasa na kasar Masar, Khalid Abd El-aziz, ya bayyana fatan cewa shahararren dan wasan kwallon kafa na kasar Mohammed Salah zai buga gasar kwallon kafa ta duniya da za gudanar a kasar Rasha duk kuwa da rauni da ya samu a kafadarsa a jiya Asabar.
-
Masar Ta Yaba Da Tattaunawar Aljeriya Kan Rikicin Libiya
May 24, 2018 06:47Ministan harakokin wajen Masar ya yaba da tattaunawar da makwabtar Libiya suke yi a Aljeriya domin lalubo hanyar magance rikicin kasar Libiya
-
Human Rights Watch Ta Yi Soka Kan Wuce Gona Da Irin Sojojin Masar A Sina
May 22, 2018 14:51Kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Human Rights Watch ta bayyana cewa: Matakan da sojojin gwamnatin Masar suke dauka da sunan yaki da ta'addanci a yankin Sina sun yi hannun riga da dokoki.
-
Gwamnatin Masar Tana Ci Gaba Da Kame 'Yan Adawar Siyasa
May 21, 2018 07:33Mahukunta Masar sun bada umurnin tsare wani dan adawar siyasa kan zargin alaka da kungiyar ta'addanci a kasar.
-
Ma'aikatar Harkokin Wajen Sudan Ta Kirayi Jakadan Masar Domin Bayyana Masa Kokenta
May 20, 2018 07:44Ma'aikatar harkokin wajen Sudan ta kirayi jakadan Masar da ke kasarta domin bayyana masa rashin jin dadinta kan wani wasan kwaikwayo da za a nuna a wata tashar talabiji na kasar Masar.
-
Iyalan Tsohon Shugaba Morsi Sun Nuna Tsananin Damuwarsu Kan Halin Da Yake Ciki
May 19, 2018 13:24Iyalan hambararren shugaban kasar Masar Muhammad Morsi sun bayyana tsananin damuwarsu dangane da mawuyacin halin da yake ciki a inda ake tsare da shi.
-
Tashin Bom Ya Ritsa Da Babban Kwamandan Rundunar Tsaron Lardin Sina Na Masar
May 18, 2018 07:24Wani bom ya tashi a kan hanyar shigewar tawagar babban kwamandan rundunar tsaro a lardin Sina ta Arewa da ke kasar Masar.
-
Rundunar Sojin Masar Ta Sanar Da Kame 'Yan Ta'adda 19 A Yankin Sina Na Kasar
May 17, 2018 07:22A wani samame da rundunar sojin Masar ta gudanar a yankin Sina na kasar ta yi nasarar cafke 'yan ta'adda 19.
-
Sojojin Masar Sun Halaka 'Yan Ta'adda 21 A Yankin Sinai
May 10, 2018 22:09A ci gaba da kaddamar da farmakin da dakarun gwamnatin Masar ke a yankin Sinai, sun sanar da halaka 'yan ta'adda 21 a yankin tare da kame wasu.
-
An Gagara Cimma Matsaya A Taron Magance Matsalar Madatsar Ruwan Kasar Ethiopia
May 08, 2018 06:42Ministan harkokin wajen kasar Masar ya bayyana cewar har ya zuwa yanzu dai an gagara cimma wani abin a zo a gani a taron tattaunawa tsakanin kasar Masar, Sudan da Ethiopia don magance rikicin da ya kunno kai a tsakaninsu dangane da madatsar ruwar da kasar Ethiopia take ginawa a kan Tekun Nilu.