An Gagara Cimma Matsaya A Taron Magance Matsalar Madatsar Ruwan Kasar Ethiopia
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i30636-an_gagara_cimma_matsaya_a_taron_magance_matsalar_madatsar_ruwan_kasar_ethiopia
Ministan harkokin wajen kasar Masar ya bayyana cewar har ya zuwa yanzu dai an gagara cimma wani abin a zo a gani a taron tattaunawa tsakanin kasar Masar, Sudan da Ethiopia don magance rikicin da ya kunno kai a tsakaninsu dangane da madatsar ruwar da kasar Ethiopia take ginawa a kan Tekun Nilu.
(last modified 2018-08-22T07:01:48+00:00 )
May 08, 2018 06:42 UTC
  • An Gagara Cimma Matsaya A Taron Magance Matsalar Madatsar Ruwan Kasar Ethiopia

Ministan harkokin wajen kasar Masar ya bayyana cewar har ya zuwa yanzu dai an gagara cimma wani abin a zo a gani a taron tattaunawa tsakanin kasar Masar, Sudan da Ethiopia don magance rikicin da ya kunno kai a tsakaninsu dangane da madatsar ruwar da kasar Ethiopia take ginawa a kan Tekun Nilu.

Kamfanin dillancin labaran Reuters, ya jiyo Sameh Al-Shoukry, ministan harkokin wajen kasar Masar din, ya bayyana cewar taron da kwararrun kasashen da ke rikicin suka gudanar bai cimma wani abin a zo a gani wajen magance matsalar ba.

Rikici dai ya kunno kai ne tsakanin Masar da Ethiopia dangane da ci gaba da gina madatsin ruwa Dala Biliyan 4 da kasar Ethiopian take ginawa a Tekun na Nilu wanda Masar din ta ce hakan zai rage irin ruwan da ke isa bangarenta wanda zai haifar mata ta matsala.

Har ila yau kuma kasar Masar din tana rikici da kasar Sudan sakamakon goyon bayan gina madatsar ruwa da ta yi wanda a cewarta zai taimaka mata wajen magance matsalar wutar lantarki da take fama da ita.