-
Malaman Jami'ar Azhar Ta Masar Sun Bukaci Karfafa Palasdinawa Domin Ci Gaba Da Bore
Dec 13, 2017 08:17Kwamitin manyan malaman jami'ar Azhar ta Masar ya bukaci tallafawa al'ummar Palasdinu da kudade domin samun damar ci gaba da gudanar da boren da suke yi na kare birnin Qudus.
-
An Kama Wasu Masu Zanga-Zangar Yin Allah Wadai Da Amurka A Kasar Masar
Dec 12, 2017 02:57Wani babban lauya a kasar Masar ya bada sanarwan cewa jami'an tsaro a birnin Al-Kahira sun kama wasu daga cikin wadanda suka gudanar da zanga-zangar yin Allahwadai da shugaban kasar Amurka kan abin da ya shafi birnin Qudus.
-
Rasha : Putin Ya Fara Ziyara A Masar
Dec 11, 2017 12:05Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya fara wata ziyarar aiki a birnin Alkahira na kasar Masar.
-
Jami'ar Azhar Ta Kasar Masar Ta Bukaci Shirya Taron Kasa Da Kasa Kan Birnin Qudus
Dec 10, 2017 15:38Jami'ar Azhar ta kasar Masar ta yi gargadi kan irin mummunan hatsarin da ke tattare da matakin da shugaban kasar Amurka ya dauka na shelanta birnin Qudus a matsayin fadar mulkin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila, don haka ta bukaci shirya zaman taron kasa da kasa kan batun na Qudus.
-
Shugaban Kiristoci Kibdawa Na Masar Ya Soke Ganawa Da Mataimakin Shugaban Amurka Saboda Batun Qudus
Dec 09, 2017 13:30Paparoman Kibdawan kasar Masar, Paparoma Tawadros II ya soke shirin ganawa da mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence da a baya aka shirya yi a wani lokaci a watan nan a birnin Alkahira don nuna rashin amincewarsa ga matsayar da shugaban Amurkan ya dauka na bayyanar birnin Qudus a matsayin babban birnin haramtacciyar kasar Isra'ila.
-
Matsayin Qudus : Limamin Al-Azhar Ya Soke Ganawarsa Da Mataimakin Trump
Dec 09, 2017 02:23Babban limamin jami'ar Al-Azhar na kasar Masar, Ahmed al-Tayeb, ya soke ganawarsa da mataimakin shugaban Amurka, Mike Pence, a matstayin maida martani kan matakin Trump na ayyana Qudus babban birnin Isra'ila.
-
An Yanke Hukuncin Kisa Kan Wasu 'Yan Ta'adda 13 A Masar
Dec 07, 2017 15:29Kotun kasar Masar ta yanke hukuncin kisa kan wasu mutane 13 da ta same su da laifin aikata ta'addanci a kasar
-
Tsohon Fira Ministan Masar Ya Ce Mahukuntan Kasar Hadaddiyar Daular Larabawa Ba Su Tsare Shi Ba
Dec 04, 2017 03:27Tsohon fira ministan Masar Ahmed Shafiq ya bayyana cewa babu gaskiya a labarin cewa: Mahukuntan kasar Hadaddiyar Daular Larabawa sun tsare shi saboda shirinsa na tsayawa takarar shugabancin kasa a Masar a zaben shekara ta 2018.
-
Masar Ta Bayyana Damuwarta Kan Dawowar 'Yan Kungiyar Da'ish Zuwa Yankin Arewacin Afrika
Dec 04, 2017 03:26Ministan harkokin wajen kasar Masar ya bayyana tsananin damuwarsa kasarsa kan yiyuwar dawowar 'yan kungiyar ta'addanci ta Da'ish zuwa yankin arewacin Afrika bayan kashin da suka sha a kasashen Siriya da Iraki.
-
Iyalan Tsohon Firayi Ministan Masar Sun Ce Ba Su San Inda Yake Ba Bayan Dawowarsa Gida
Dec 03, 2017 07:50Iyalan tsohon firayi ministan kasar Masar Ahmad Shafik sun bayyana cewa ba su da wani labari kan wajen da ya ke tun bayan da gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa suka taso keyarsa zuwa kasar Masar din tun bayan da ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin kasar.