Rasha : Putin Ya Fara Ziyara A Masar
https://parstoday.ir/ha/news/world-i26251-rasha_putin_ya_fara_ziyara_a_masar
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya fara wata ziyarar aiki a birnin Alkahira na kasar Masar.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Dec 11, 2017 12:05 UTC
  • Rasha : Putin Ya Fara Ziyara A Masar

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, ya fara wata ziyarar aiki a birnin Alkahira na kasar Masar.

A yayin ziyarar tasa Mista Putin ya gana da takwaransa na Masar Abdel Fattah al-Sissi, inda suka tattauna kan batutuwa da dama, ciki har da halin da ake ciki a Qudus bayan da shugaba Trump na Amurka ya ayyanasa a matsayin babban birnin yahudawan sahayoniya 'yan mamaya.

Bayanai daga kasar sun kuma ce bangarorin biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyar karshe ta gina tashar wutar lantarki ta farko mai aiki da makamashin nukiliya a kasar ta Masar.

Tashar ta Dabaa wacce zata samar da wutar lantarki mai karfin Migawatt 1.200 an dai cimma yarjejeniya gina ta ne a watan Nuwamba 2015.

A tsakiyar ranar yau Litini ce shugaba Putin ya isa kasar ta Masar bayan wata ziyara ba zata a kasar Siriya.