Matsayin Qudus : Limamin Al-Azhar Ya Soke Ganawarsa Da Mataimakin Trump
Babban limamin jami'ar Al-Azhar na kasar Masar, Ahmed al-Tayeb, ya soke ganawarsa da mataimakin shugaban Amurka, Mike Pence, a matstayin maida martani kan matakin Trump na ayyana Qudus babban birnin Isra'ila.
A cikin wata sanarwa da Ahmed al-Tayeb ya fitar ya ce ya yi watsi da bukatar ta Mista Pence wanda aka tsara zasu ganawa a wata ziyara a kasar ta Masar a ranar 20 ga watan nan
Babban limamin na Al-Azhar, ya yi tir da allawadai da kakkausar murya dangane da matakin shugaba Trump na mayar da ofishin jakadamcin Amurka zuwa Qudus da kuma ayyanasa a mastayin babban birnin yahudawan sahayoniya 'yan mamaya na Isra'ila.
Sanarwar da Al'Azhar ta fitar ta ce a makon da ya gabata ne Amurka ta aike mata da bukatar neman ganawar mataimakin shugaban kasar Mike Pence da babban Limanin kuma ta amince, amma biyo bayan matakin Amurka marar adalci kan birnin Qudus ta soke ganawar.