-
Kudaden Shigar Da Gwamnatin Masar Take Samu A Mashigar Ruwa Ta Suez Ya Karu
Aug 06, 2017 12:50Kudaden shiga wadanda gwamnatin kasar Masar take samu a mashigar ruwa ta suez ya kai dalar Amurka milion 446.3 a cikin watan Yulin da ya gabata daga dalar miliyon $427.2 a cikin watan yuni.
-
Kasashen Aljeriya Da Masar Sun Jaddada Bukatar Taimakekkeniya A Fagen Yaki Da Ta'addanci
Aug 02, 2017 13:48Ministocin harkokin wajen kasashen Aljeriya da Masar sun jaddada bukatar karfafa taimakekkeniya a tsakaninsu a fagen yaki da ayyukan ta'addanci tare da jaddada wajabcin samun hadin kan duniya da nufin warware rikicin kasar Libiya.
-
Rusa Wata Maboyar 'Yan Ta'adda A Lardin Tsibirin Sina Da Ke Kasar Masar
Aug 02, 2017 13:47Rundunar sojin Masar ta sanar da rusa wata maboyar 'yan ta'adda a lardin Tsibirin Sina na kasar.
-
Kotun Masar Ta Wanke Dan 'Uwan Shugaban AlQa'ida.
Aug 01, 2017 08:31Wata Kotu a Masar ta wanke dan'uwan shugaban kungiyar ta'addancin nan ta alka'ida kan zarkin da ake yi masa na kafa kungiyar masu tsatsauran ra'ayin addini.
-
Tsohon Muftin Kasar Masar Ya Gargadi Musulmi
Jul 31, 2017 10:07Tsohon muftin kasar masar kuma babban malami addini a kasar ya yi kira ga musulmi su yi hattara da bin tsarin karantarwa na kasashen yamma wanda aka gina kan kiyayya ga addinin musulunci.
-
Masar: Daurin Rai Da Rai A Kan 'Yan Kungiyar Musulim Brotherhood Su 58
Jul 28, 2017 14:23Kotun soji a kasar Masar ta yanke hukuncin daurin rai da rai a kan wasu magoya bayan kungiyar Muslim Brotherhood su 58, bisa zarginsu da kai hari a kan wuraren tsaro a lokacin da aka hambarar da Muhammad Morsi.
-
An Kona Tutar Haramtacciyar Kasar Isra'ila A Masar
Jul 28, 2017 08:57Wasu 'yan siyasa da kungiyoyin fararen hula sun gudanar da taron goyon bayan Masallacin Aksa a cibiyar kungiyar 'yan jaridun Masar tare da kone tutar HKI.
-
Masar Ta Kafa Majalisar Kasa Ta Fada Da Ta'addanci A Kasar
Jul 27, 2017 00:58Gwamnatin kasar Masar ta sanar da kafa wata majalisa ta kasa mai karfin iko don fada da ta'addanci da cikin shekarun nan yake ci gaba da barazana ga tsaro da zaman lafiyan kasar.
-
Wata Kotu A Masar Ta Yanke Hukuncin Daurin Rai-da-Rai Kan Yan Adawa 43
Jul 25, 2017 11:05Wata kotu a kasar Masar ta yanke hukuncin daurin rai-da-rai kan wasu yan adawa da gwamnatin kasar su 43 a yau Talata.
-
Farashin Kudin Kujerar Hajjin Bana Ya Yi Tashin Gwabron Zabi A Masar
Jul 25, 2017 08:25Al'ummar kasar Masar suna kokawa matuka dangane da karin farashin kujerar hajjin bana da hukumar alhazi ta kasar ta yi.