Farashin Kudin Kujerar Hajjin Bana Ya Yi Tashin Gwabron Zabi A Masar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i22566-farashin_kudin_kujerar_hajjin_bana_ya_yi_tashin_gwabron_zabi_a_masar
Al'ummar kasar Masar suna kokawa matuka dangane da karin farashin kujerar hajjin bana da hukumar alhazi ta kasar ta yi.
(last modified 2018-08-22T07:00:27+00:00 )
Jul 25, 2017 08:25 UTC
  • Farashin Kudin Kujerar Hajjin Bana Ya Yi Tashin Gwabron Zabi A Masar

Al'ummar kasar Masar suna kokawa matuka dangane da karin farashin kujerar hajjin bana da hukumar alhazi ta kasar ta yi.

Shafin yada labarai na Almisrawi ya bayar da rahoton cewa, farashin kudin kujerar aikin hajjin bana a kasar masar ya ninka har sau kusan biyu da rabi idan aka kwatanta da farashin shekarar da ta gabata.

Rahoton ya ce al'ummar kasar suna ta kokawa matuka kan wannan lamari, inda tuni wakilan jama'a  amajalisar dokokin kasar siuka gabatar da wannan magana da nufin neman yin sassaucin a kan lamarin.

Sai dai a nasa bangaren babban daraktan hukumar alhazai ta kasar Aiman Sami ya bayyana cewa, ba da son ransu ne hakan ke faruwa ba, domin kuwa mahukuntan Saudiyya ne suka kara musu yawan kudaden haraji da suke karba daga kamfanonin jigilar alhazai, kamar yadda hatta kudaden biza sun ninka kusan sau uku, inda ya ce wannan lamari yana a matsayin wata annoba.