Jul 31, 2017 14:37 UTC
  • Tsohon Muftin Kasar Masar Ya Gargadi Musulmi

Tsohon muftin kasar masar kuma babban malami addini a kasar ya yi kira ga musulmi su yi hattara da bin tsarin karantarwa na kasashen yamma wanda aka gina kan kiyayya ga addinin musulunci.

Kamfanin dillancin labaran RASA ya nakalto Sheikh Ali Juma'ah yana fadar haka a yau litinin, ya kuma kara da cewa zuwan musulmi kasashen yamma don jawo hankalin matasansu yana da hatsari idan sun bi tsarin karantarwa da wadan nan kasashe. Sheikh Jumu'ah ya ce su yi hattara da tsarin karantarwa na wadan nan kasashe wanda aka gina shi bisa nuna adawa da kuma kin musulunci da musulmi

Sheikh Jumu'ah ya ce kasashen yamma suna ganin cewa ci gaba yana wajensu ne su kadai, banda haka sun dauki cewa ci gaba na samuwa ne kadai ta hanyar 'yanci da barin mutane su yi abinda suka ga dama, ba tare da takaitasu ba. 

Malamin ya bayyana haka ne a shafinsa na facebook, ya kuma kara da cewa musulmi suna da karantarwar al-qur'ani mai girma da kuma na manzon Allah (s), wadanda suka game kome da kome a cikin rayuwar bil'adama, idan da musulmi zasu bi umurnin Allah kamar yadda yakamata, da kuwa ba'a bukatar 'yansanda da jami'an tsaro don tursasawa mutane aikata alkhairi kuma hanasu sharri. 

Daga karshe malamin ya kara da cewa a cikin yan shekarun da suka gabata, an rubuta litattafai kimani 3,600 wadanda suke sukan da kuma nuna kiyayya ga musulmi da kuma addinin musulunci a kasashen yamma.

 

Tags