Pars Today
Akalla mutane 20 ne masu satar danyen man fitur daga bututan man a karkashin kasa suka halaka a kasar Mexico a jiya Jumma'a
Gwamnatin kasar Mexico ta ki amincewa da bukatar kungiyar Lima ta kasashen yankin Laten Amurka na bukatar shugaban kasar Venezuela ya sauka kan mukaminsa na shugaban kasarsa.
Wasu jerin fashe -fashe a wani wajen sayar da kayayyakin wasan wuta a kasar Mexico sun lashe rayukan mutane akalla 24 tare da jikkata wasu fiye da 30 na daban.
A Mexico, dan takarar masu ra'ayin kawo sauyi, Andres Manuel Lopez Obrador, ya lashe zaben shugaban kasar, wannan shi ne karon farko da wani dan takara mai wannan ra'ayin ya lashe zaben wannan kasa.
Shugaban kasar Mexico Enrique Peña Nieto ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta taba biyan kudade don gina katanka tsakanin kasar da kasar Amurka ba.
Ma'aikatar shari'ar kasar Mexico ta sanar da kame shahararren mai fataucin muggan kwayoyi a kasar da ake zargi da hannu a kashe daliban makaranta 43 a shekara ta 2014.
Hukumomin shari'a a jihar Oaxaca a kudancin Mexico, sun ce mutum 13 ne suka gamu da ajalinsu a yayin da wani jirgi mai saukar ungulu na ministan cikin gida na kasar, Alfonso Navarrete, dake kan hanyar zuwa yankin da girgiza kasa ta auka ma a jiya Juma'a ya yi hadari.
Majalisar Dinkin Duniya da gwamnatin kasar Mexico sun koka kan yadda ake ci gaba da samun bullar kashe-kashen gilla kan 'ya'ya mata a kasar ta Mexico.
Rahotanni daga Mexico na cewa mutane sama da 200 ne suka rasa rayukansu a mummunar girgiza kasar data aukawa kasar a jiya Talata.
A cikin wani bayani da majalisar musulmin kasar Birtaniya ta fitar ta yi gargadi dangane da yadda kyamar musulmi ke ci gaba da karuwa a kasar.