Girgiza Kasa Ta Kashe Mutum 224 A Mexico
Rahotanni daga Mexico na cewa mutane sama da 200 ne suka rasa rayukansu a mummunar girgiza kasar data aukawa kasar a jiya Talata.
Kawo yanzu dai alkalumman wucin gadi da hukumomin kasar suka fitar sun nuna cewa mutane 224 ne suka rasa rayukansu a mummunar girgizar kasar mai karfin maki 7.1 bisa ma'aunin Richter.
Girgizar kasar dai ta yi barna sosai a galibin yankunan dake tsakiyar kasar ciki har babban birnin kasar.
Wannan ita ce girgiza kasa mafi muni da kasar ta fuskanta cikin shekaru 32 da suka wuce bayan wacce ta yi ajalin mutane sama da dubu guda a shekara 1985.
Kazalika wannan shi ne karo na biyu da aka yi girgizar kasa a kasar ta Mexico cikin makwanni biyu, bayan aukuwar girgizar kasa mai karfin maki 8.2 a yankin gabar ruwa dake kudancin kasar a ranar 7 ga wannan wata.