Majalisar Musulmin Birtaniya Ta Yi Gargadi Dangane Da Karuwar Kyamar Musulmi
A cikin wani bayani da majalisar musulmin kasar Birtaniya ta fitar ta yi gargadi dangane da yadda kyamar musulmi ke ci gaba da karuwa a kasar.
shafin yada labarai na IINA ya bayar da rahoton cewa, jami’an ‘yan sandan kasar Birtaniya sun fitar da wani rahoto da ke tabbatar da karuwar kin jinin musulmi a yankuna daban-daban na kasar ta Birtaniya , tun bayan kaddamar da harin da kungiyar ‘yan ta’addan ISIS ta yi a biranan London da kuma Manchester.
A nata bangaren majalisar musulmin kasar ta Birtaniya ta fitar da nata jawabin da ke cewa, tun bayan kai hare-haren na London da Manchester, kyamar musuli da cin zarafinsu da kuma yin barazana a kansu na karuwa.
Harun Khan babban sakataren majalisar musulmin Birtaniya ya bayyana cewa, wannan lamari ne mai matukar hadari, domin kuwa a halin yanzu musulmi a kasar Birtaniya suna fuskantar barazana daga wasu masu tsanannin kiyayya da addinin muslunci, bisa hujjar cewa musulmi ne suke kaddamar da hare-haren ta’addanci.
Harun Khan ya bayar da misalin harin da aka kai a kan musulmi a Finsbury Park bayan kammala salla, ya ce babu wani dalili da masu kai irin wadannan hare-hare kan musulmi za su fake da su.
Daga karshe ya kirayi gwamnatin Birtaniya da kuma jami’an tsaro da suka fitar da wannan rahoto a kan cewa su sauke nauyin da ya ratay a kansu na kare rayukan msulmi da dukiyoyinsu da kuma mutuncinsu.