-
FIFA Da Kungiyar Man. UTD Sun Nuna Alhini Mutuwar Magoya Bayan Man United A Nijeriya
Apr 22, 2017 01:16Hukumar kwallon kafa ta duniya (FIFA) da kuma kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta kasar Ingila sun bayyana bakin ciki da kuma aihininsu dangane da mutuwar wasu magoya bayan kungiyar su kimanin 30 a birnin Calabar, na Jihar Cross River da ke kudancin Nijeriya sakamakon fadowar wani layin wutar lantarki a kansu.
-
Shugaba Jonathan Ya Amince Da Bayar Da Naira Billiyan 15 Dan Zaben 2015-Tsohon Daraktan NIA
Apr 21, 2017 07:48Wani tsohon diraktan hukumar leken asiri ta Nijeriya wato NIA ya bayyana cewa tsahon shugaban kasar Goodluck Jonathan ya bayar da naira billiyan 15 ga hukumar don rabawa 'ya'yan jam'iyyar PDP a zaben shekara ta 2015.
-
Karancin Hanyoyin Isar Da Wutan Lantarki Mai Karfin MW 12,000 Shi Ne Ke Jefa Nigeria Cikin Duhu
Apr 21, 2017 07:47Kungiyar kamfanoni masu samar da wutan lantarki wato The Association of Power Generation Companies, APGC a Nigeria ta bayyana cewa zata iya samar da wutan lantarki mai karfin mw dubu 12,000 a halin da ake ciki, amma hanyoyin rarraba wutan lantarki a kasar baya iya isar da wuta mai karfi fiye da MW 4.600 ba.
-
Sankarau Ya Kashe Mutane Fiye Da 750 A Najeriya
Apr 20, 2017 10:36Majiyar ma'aikatar kiwon lafiya a Nigeria ta bayyana cewa yawan mutanen da suka rasa rayukansu sanadiyyar cutar sankarau a wasu jihohi a kasar ya daga zuwa 750.
-
Shugaba Buhari Ya Bada Umurnin A Binciki Wani Babban Jami'i Kan Karkatar Da Kudaden Yan Gudun Hujira
Apr 20, 2017 10:32Shugaban tarayyar Nigeria ya bada umrni na a gudanar da bincike kan karkata kudaden tallafawa yan gudun hijira daga arewa maso gabaciin kasar wanda ake zargin wani babban jami'an gwamnatinsa da yin.
-
Akwai Yiyuwar A Bincike Jonathan Kan Naira Biliyan 13 Da EFCC Ta Gano A Lagos
Apr 20, 2017 06:53Wasu majiyoyin labarai sun bayyana cewar akwai yiyuwar kwamitin da shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya kafa don binciko kimanin Naira biliyan 13 da hukumar EFCC mai fada da ta'annuti ga tattalin arzikin kasar ta gano a Lagos ya gayyaci tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan, gwamnan babban bankin kasar Godwin Emefiele da kuma shugaban EFCC din don neman karin bayani daga wajensu.
-
Najeriya : An Bude Filin Jiragen Sama Na Abuja
Apr 19, 2017 00:55Rahotanni daga Najeriya na cewa jiragen sama sun soma sauka da tashi a filin jirgin saman kasa da kasa na N'namdi Azikiwe dake Abuja, bayan kwashe makwanni shida a rufe sakamakon aikin gyaran hanyoyin saukar jiragen.
-
Najeriya : An Bude Filin Jirgin Saman Abuja
Apr 19, 2017 00:51Rahotanni daga Najeriya na cewa jiragen sama sun soma sauka da tashi a filin jirgin saman kasa da kasa na N'namdi Azikiwe dake Abuja, bayan kwashe makwanni shida a rufe sakamakon aikin gyaran hanyoyin saukar jiragen.
-
Sojojin Nijeriya Sun Sami Nasarar Hallaka Wasu 'Yan Kungiyar Boko Haram 21
Apr 18, 2017 06:33Rundunar sojin Nijeriya ta ce sojojinta sun sami nasarar hallaka wasu mayakan kungiyar Boko Haram su 21 da kuma ceto wasu mutane 1,623 da 'yan ta'addan suka yi garkuwa da su bayan wani gumurzu a kauyen Jarawa na karamar hukumar Kale Balge da ke jihar Borno.
-
NCAA: Gobe Laraba Za'a Bude Filin Jirgin Saman Abuja
Apr 18, 2017 06:32Babban daraktan hukumar safarar jiragen sama ta Nijeriya (NCAA) Usman Muktar ya sanar da cewa an kammala ayyukan da ake yi a titunan sauka da tashin jiragen sama a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, don haka za a bude filin jirgin sama a gobe Laraba.