Najeriya : An Bude Filin Jiragen Sama Na Abuja
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19578-najeriya_an_bude_filin_jiragen_sama_na_abuja
Rahotanni daga Najeriya na cewa jiragen sama sun soma sauka da tashi a filin jirgin saman kasa da kasa na N'namdi Azikiwe dake Abuja, bayan kwashe makwanni shida a rufe sakamakon aikin gyaran hanyoyin saukar jiragen.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Apr 19, 2017 05:25 UTC

Rahotanni daga Najeriya na cewa jiragen sama sun soma sauka da tashi a filin jirgin saman kasa da kasa na N'namdi Azikiwe dake Abuja, bayan kwashe makwanni shida a rufe sakamakon aikin gyaran hanyoyin saukar jiragen.

An dai bude filin jirgi ne a jiya Talata wato kwana guda kafin wa'adin da aka dauka, kuma jirgin saman Ethiopian Airline ne ya share fagen sauka da tashin jiragen.

An dai kammala aikin 100% a cewar shugaban hukumar kula da sufurin jiragen saman kasar Hadi Sirika a shaffinsa na Twitter, wanda a cewarsa babbar nasara ce gwamnatin kasar.

Marabin dai da'a yi irin wannan gyaran tun gina filin jirgin a shekara 1982, lamarin daya kasance babban hadari ga yanayin hanyoyin saukar jiragen.

Bayan rufe filin jirgin na Abuja a ranar 8 ga watan jiya an karkata akalar sauka da tashin jiragen saman kasa da kasa zuwa jihar Kaduna dake arewacin kasar, matakin da wasu kamfanonin jiragen sama irinsu Air France, Lufthansa, da South African Airways suka ce basu lamunta dashi ba saboda dalilai na tsaro.