Sankarau Ya Kashe Mutane Fiye Da 750 A Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19632-sankarau_ya_kashe_mutane_fiye_da_750_a_najeriya
Majiyar ma'aikatar kiwon lafiya a Nigeria ta bayyana cewa yawan mutanen da suka rasa rayukansu sanadiyyar cutar sankarau a wasu jihohi a kasar ya daga zuwa 750.
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Apr 20, 2017 10:36 UTC
  • Sankarau Ya Kashe Mutane Fiye Da 750 A Najeriya

Majiyar ma'aikatar kiwon lafiya a Nigeria ta bayyana cewa yawan mutanen da suka rasa rayukansu sanadiyyar cutar sankarau a wasu jihohi a kasar ya daga zuwa 750.

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa daga birnin Lagos ya bayyana cewa a cikin makonni biyu da suka gabata mutane 300 suka rasa rayukansu sanadiyyar cutar. 

Majiyar ta kara da cewa mutane 8,057 suka kama da cutar tun farko bullarta a cikin watan Maris da ya gabata, kuma mafi yawan wadanda suka kamun sun fito ne daga  jihohin Zamfara Sokoto Katsina Kebbi da Niger.

Dr John Oladejo shugaban kula da kiwon lafiya ta The National Primary Health Care Development Agency (NPHCDA) ya yabawa likitocin da suka bada lokacinsu musamman a cikin hutun Easter don tallafawa aikin yin alluran riga kafi a wadan nan jihohi.