-
Sheikh Siddiqi: Saudiyya Da Kawayenta Sun Gaza Cimma Manufarsu A Siriya
Aug 26, 2016 12:29Wanda ya jagoranci sallar Juma'ar birnin Tehran ya bayyana cewar Saudiyya ta gaza wajen cimma manufarta na kifar da gwamnatin Siriya da kuma yadda ayyukan ta'addanci duk kuwa da irin kudi da farfagandar da ta yi amfani da su, yana mai cewa ko shakka babu sahyoniyawa da 'yan ta'adda za su sha kashi a kasar Siriyan.
-
Dan Bin Laden, Ya Bukaci A Kawar Da Masarautar Saudiyya
Aug 18, 2016 06:42Dan Osama Bin Laden, ya yi kira ga al’ummar kasar Saudiyya da su kawo karshen mulkin gidan sarautar Ali Sa’ud domin ‘yantar da kansu daga mamayar Amurka.
-
Nuri Al-Maliki: Saudiyya Ita Ce Tushen Ayyukan Ta'addanci Da Wajibi Ne A Dau Mataki Kanta
Aug 14, 2016 12:52Tsohon firayi ministan kasar Iraki Nuri al-Maliki ya bayyana kasar Saudiyya a matsayin tushe kana kuma mabubbugar ta'addanci wanda wajibi ne kasashen duniya su dau mataki kanta
-
An Sami Karuwar 'Isra'ilawa' Da Suke Kai Ziyara Saudiyya Da Sauran Kasashen Larabawa
Aug 12, 2016 00:32Rahotanni ne sun ce an sami karuwar adadin 'Isra'ilawa' da suke kai ziyara kasar Saudiyya, kasashen larabawan Tekun Fasa da kuma kasar Masar tun a farkon shekarar nan lamarin da ke nuni da kokarin da wasu kasashen larabawan musamman Saudiyya take yi na kulla alaka a bayyana da haramtacciyar kasar Isra'ila.
-
Bincike: Sama Da 'Yan Ta'adda Dubu 360 Daga Kasashe 93 Aka Shigar Da Su Siriya
Aug 08, 2016 13:26Cibiyar binciken nan ta Farrell ta kasar Jamus ta sanar da cewa tun daga shekara ta 2011 da aka fara rikici a kasar Siriya ya zuwa yanzu an shigar da 'yan ta'adda sama da dubu 360 da suka fito daga kasashe sama da 93 na duniya zuwa kasar.
-
Saudiyya Ta Fara Kwashe Mutanen Garuruwan Kan Iyaka Da Yemen Bayan Nasarorin Dakarun Yemen
Aug 05, 2016 05:43Kasar Saudiyya ta kaddamar da wani shiri na kwace mutanen yankin Jizan na kasar da ke makwabtaka da kasar Yemen biyo bayan ci gaba da kutsawa cikin kasar Saudiyyan da sojojin kasar Yemen suke yi a matsayin mai da martani da hare-haren wuce gona da irin sojojin Saudiyyan da kawayenta a kan al'ummar kasar Yemen.
-
Iran: Kin Sanya Saudiyya Cikin Masu Take Hakkokin Yara, Ha'inci Ne Ga Yaran Yemen
Aug 03, 2016 06:44Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewar kin sake sanya kasar Saudiyya cikin jerin sunayen kasashen da ke take hakkokin yara sakamakon kisan gillan da take yi wa yaran kasar Yemen da MDD ta yi cin amanar kananan yaran Yemen din ne.
-
Sayyid Nasrallah Yayi Kakkausar Suka Ga Kokarin Saudiyya Na Kulla Alaka Da "Isra'ila"
Jul 29, 2016 12:52Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyid Hasan Nasrallah yayi kakkausar suka ga kokarin da kasar Saudiyya take yi na kusatar haramtacciyar kasar Isra'ila da kulla alaka da ita, yana mai kiran al'ummar musulmi da su yi Allah wadai da duk wani kokari na kusatar haramtacciyar kasar Isra'ila da yin watsi da matsalar Palastinu.
-
Tawagar Jami'an Saudiyyah A Haramtacciyar Kasar Isra'ila
Jul 24, 2016 03:49A cikin wannan mako ne wata tawagar kasar Saudiyyah karkashin jagorancin Anwar Ishki, wani tsohon janar na sojin sojin Saudiyya, kuma tsohon shugaban bangaren ayyukan leken asiri na soji a kasar, wanda ke jagorantar wata cibiyar bincike kan harkokin tsaro a halin yanzu a birnin Jidda.
-
Masarautar Ali-Saud Ta Haramta Wa Maniyyatan Syria Zuwa Aikin Hajjin Bana
Jul 22, 2016 12:34Sarakunan masarautar iyalan gidan Saud sun hana musulmi maniyyata daga kasar Syria zuwa aikin bana, ta hanyar hana su izinin shiga kasar (visa) ba tare da bayyana wani dalili na yin hakan ba.