Dan Bin Laden, Ya Bukaci A Kawar Da Masarautar Saudiyya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i9811-dan_bin_laden_ya_bukaci_a_kawar_da_masarautar_saudiyya
Dan Osama Bin Laden, ya yi kira ga al’ummar kasar Saudiyya da su kawo karshen mulkin gidan sarautar Ali Sa’ud domin ‘yantar da kansu daga mamayar Amurka.
(last modified 2018-08-22T06:58:47+00:00 )
Aug 18, 2016 06:42 UTC
  • Dan Bin Laden, Ya Bukaci A Kawar Da Masarautar Saudiyya

Dan Osama Bin Laden, ya yi kira ga al’ummar kasar Saudiyya da su kawo karshen mulkin gidan sarautar Ali Sa’ud domin ‘yantar da kansu daga mamayar Amurka.

Hamza dan shekaru 23, wanda dan lele ne ga marigayi Osama Bin Laden wanda ya kafa kungiyar Al'Qaida ya yi kira ga matasa a kasar Saudiya da su shiga kungiyar Al Qaeda reshen kasar Yemen domin koyan dabarun yaki don kifar da mulkin Al'Saud.

Dama a lokacin da yake raye Osama Bin Laden, ya yi ta fatan dan sa Hamza ya gaje shi a shugabancin kungiyar 'yan ta'adan ta Al'Qaida.

Shekaru biyar dai bayan da sojin Amurka suka kashe Osama Bin Laden a Pakistan, har yanzu dai sunansa na zamen babbar barazana ga Saudiyya da Amurka.

Osama Bin Laden dai shi ne dai wanda ake zargi da hannu wajen shirya harin da aka kai wa Amurka a ranar 11 ga watan Satumba 2001.