Sheikh Siddiqi: Saudiyya Da Kawayenta Sun Gaza Cimma Manufarsu A Siriya
(last modified Fri, 26 Aug 2016 16:59:11 GMT )
Aug 26, 2016 16:59 UTC
  • Sheikh Siddiqi: Saudiyya Da Kawayenta Sun Gaza Cimma Manufarsu A Siriya

Wanda ya jagoranci sallar Juma'ar birnin Tehran ya bayyana cewar Saudiyya ta gaza wajen cimma manufarta na kifar da gwamnatin Siriya da kuma yadda ayyukan ta'addanci duk kuwa da irin kudi da farfagandar da ta yi amfani da su, yana mai cewa ko shakka babu sahyoniyawa da 'yan ta'adda za su sha kashi a kasar Siriyan.

Hujjatul Islam wal Muslimin Sheikh Kazim Siddiqi ya bayyana hakan ne a yau din nan a lokacin da yake gabatar da hudubar sallar Juma'a a nan Tehran inda ya ce baya ga  kashin da Saudiyya da kawayenta suke sha a fagen daga a Siriyan har ila yau kafafen watsa labaran Saudiyyan sun gaza wajen cimma manufarsu ta kokarin bayyana abin da ke faruwa a Siriya a matsayin wani yaki ne na neman 'yanci yana mai cewa a halin yanzu ya bayyana wa duniya cewa abin da ke faruwa wani kokari ne kawai na yada ta'addanci da gwamnatin Saudiyyan take yi.

Har ila yau na'ibin limamin Juma'ar na Tehran ya kara da cewa abin da ke faruwa a Siriya ya tabbatar da tasirin gwagwarmaya da tsayin daka, yana mai cewa ko shakka babu a halin yanzu 'yan ta'adda suna ci gaba da diban kashinsu a hannu a Siriya duk kuwa da goyon bayan da masu tada fitina suke yi.

Yayin da ya koma kan abin da ke faruwa a Yemen kuwa, Sheikh Siddiqi ya jinjinawa al'ummar Yemen din sakamakon tsayin dakan da suka yi yana mai cewa kafa majalisar koli ta siyasa da al'ummar kasar suka kafa wani lamari ne da ke nuni da rashin nasarar da 'yan amshin shatan Saudiyya da kawayenta suke fuskanta a kokarin da suke yi na mayar da kasar 'yar amshin shata.