Pars Today
Wakilan kasashen musulmi 57 na kungiyar OIC da suka taru yau a birnin Satambul na Turkiyya sunyi tir da abunda suka kira tsokana na yahudawan mamaya na Isra'ila a masallacin Al'Aqsa dake birnin Qudus.
Shugaban bangaren siyasar kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas ya jaddada bukatar ci gaba da kokarin kare birnin Qudus da Masallacin Aksa daga mamayar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila.
Shugabannin kasashen Amurka da Turkiyya sun zanta ta hanyar wayar tarho kan rikicin da ya kunno kai tsakanin kasashen Larabawan yankin tekun Pasha a kokarin da suke yi na maida kasar Qatar saniyar ware da nufin sulhunta su.
Shugaban kasar Masar Abdul-Fatah Sisi ya bukaci kasashen duniya su dorawa gwamnatin kasar Turkiya takunkumi har zuwa lokacin da zata daina goyon bayan kasar Qatar.
Kungiyar ‘yan ta’addan ISIS ta bude wani masallaci a asirce a gabashin birnin Istanbul na Turkiya domin hada ‘yan kungiyar wuri guda a Turkiya.
Gwamnatin Turkiyya ta yi gargadin cewa zata dauki matakin ramakon gayya kan kasashen da suke goyon bayan kungiyar Fatahullahi Gulen.
A Turkiyya an fara shari'a wasu mutane sama da 200 da ake zargi da hannu a yunkurin kifar da gwamnatin shugaba Recep Tayyip Erdogan a cikin watan Yuli 2015.
Gungun 'yan ta'addan kasa da kasa da aka jibge a kasar Siriya sun harba makamai masu linzami kan yankunan da suke lardin Dire-Zur na kasar Siriya da ke kusa da kan iyaka da kasar Iraki, inda suka kashe fararen hula.
Bayanai daga Syria na cewa an samu dan sukuni a yankunan dake fama da rikice-rikice, bayan fara aiwatar da yarjejeniyar kafa tuddan mun tsira a kasar.
Shugabannin kasashen Rasha da na Turkiyya sun gana a tsibirin Sochi na kasar Rasha, inda suka tattauna harkokin da suka shafi kasashensu da ma duniya baki daya.