Shugabannin Kasashen Amurka Da Turkiyya Sun Zanta Kan Rikicin Kasashen Larabawa
(last modified Sat, 01 Jul 2017 05:42:38 GMT )
Jul 01, 2017 05:42 UTC
  • Shugabannin Kasashen Amurka Da Turkiyya Sun Zanta Kan Rikicin Kasashen Larabawa

Shugabannin kasashen Amurka da Turkiyya sun zanta ta hanyar wayar tarho kan rikicin da ya kunno kai tsakanin kasashen Larabawan yankin tekun Pasha a kokarin da suke yi na maida kasar Qatar saniyar ware da nufin sulhunta su.

Fadar White house ta sanar da cewa: Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya zanta da shugaban kasar Turkiyya Rajab Tayyib Erdogan ta hanyar wayar tarho, inda Trump ya jaddada muhimmancin ganin dukkanin kawayen Amurka sun kara matsa kaimi a fagen yaki da duk wani nau'in ayyukan ta'addanci da wuce gona da iri tare da ganin kasashen Larabawan yankin taken Pasha sun sulhunta tsakaninsu a sabon rikicin da suka bude da kasar Qatar.

Tun a ranar 5 ga watan Junin da ya gabata ne kasashen Saudiyya, Bahrain, Hadaddiyar Daular Larabawa da Masar suka sanar da yanke alakarsu ta jakadanci da kasar Qatar tare da kakaba mata takunkumin tattalin arziki bisa da'awar tana goyon bayan ayyukan ta'addanci, inda daga baya suka gindaya mata wasu jerin sharudda 13 ciki har da rufe sansanin sojin Turkiyya a cikin kasarta tare da yanke duk wata alaka da kungiyoyin gwagwarmaya irin kungiyar Hamas ta Palasdinu, kungiyar Ihwanul-Muslimin ta Masar da kuma kungiyar Hizbullahi ta Lebanon kafin su sake dawo da alaka ta ita.