Kungiyar Hamas Ta Bukaci Ci Gaba Da Kokarin Kare Masallacin Qudus
Shugaban bangaren siyasar kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas ya jaddada bukatar ci gaba da kokarin kare birnin Qudus da Masallacin Aksa daga mamayar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila.
A jawabin da ya gabatar ga al'ummar kasar Turkiyya da suke gudanar da taron gangami domin nuna goyon baya ga al'ummar Palasdinu a birnin Istambul ta hanyar hoton bidiyo kai tsaye: Shugaban bangaren siyasa na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas Isma'il Haniyya ya jaddada cewa: Birnin Qudus da Masallacin Aksa suna bukatar goyon bayan al'ummar duniya ta fuskar siyasa da dukiya domin samun damar kalubalantar bakar siyasar zaluncin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila.
Isma'il Haniyya ya kara da cewa: Har yanzu rigima tsakanin al'ummar Palasdinu musamman mazauna birnin Qudus bata kare ba tsakaninsu da sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra'ila.