Rasha, Iran, Turkiyya Na Maraba Da Ficewar Amurka A Siriya
(last modified Fri, 15 Feb 2019 04:50:47 GMT )
Feb 15, 2019 04:50 UTC
  • Rasha, Iran, Turkiyya Na Maraba Da Ficewar Amurka A Siriya

Kasashen Rasha, Turkiyya da kuma Iran, sun bayyana cewa shirin Amurka na janye dakarunta daga Siriya faduwa ce ta zo daidai da zama.

Shuwagabannin kasashen sun bayyana hakan ne a birnin Sotchi na Rasha  jiya Alhamis, a wani taronsu na duba matakan da zasu dauka bayan ficewar dakarun na Amurka daga Siriyar.

A watan Disamban shekara da ta gabata ne, shugaba Trump na Amurka, ya tabbatar da shirin janye sojojin kasarsa daga Siriya, matakin wanda kuma kasashen da suka hada da Rasha, Iran, da kuma Turkiyya suka yi maraba da shi, wanda a cewar mahukuntan Tehran kuskure ne tun farko sanya kafar Amurka a yankin.

Kasashen uku sun maida hankali ne kan yadda zasu tunkari lamarin da kuma samar da ci gaba a yankin bayan ficewar sojojin na Amurka a arewacin kasar ta Siriya, inji shugaba Vladimir Putin na Rasha.

A cewarsa mahangarmu guda ce ita ce cewa matakin na Amurka zai taimaka wajen daidaituwar al'amuran a wannan yankin na Siriya, inda daga karshe halastaciyar gwamnatin Siriya zata dauki almauran wannan yankin a hannunta.

Shi kuwa a nasa bangare, shugaba Ruhani na Iran, cewa ya yi, dole ne fa duniya ta tashi tsaye domin kawo karshen hare haren da Isra'ila ke kaiwa kan Siriya, da kuma murkushe ayyukan ta'addanci a Siriyar, sannan kuma a cewarsa a samar da hanyoyin tattaunawa  tsakanin 'yan Siriya ba tare da tsoma bakin kasashen ketare ba domin cimma zaman lafiya mai daurewa a kasar ta Siriya.