-
Al'ummar Bahrain Na Ci Gaba Da Bayar da Kariya Ga Babban Malamin Addini Na Kasar
Dec 23, 2016 17:59Al'ummar kasar Bahrain na ci gaba da bayar da kariya ga babban malamin addinin muslunci na kasar Sheikh Isa Kasim, a yunkurin da masarautar kama karya ta kasar ke yi na neman kame shi tun kimanin watannin biyar da suka gabata.
-
Demokradiyyar Congo: 'Yan sanda Sun Kame Mutane Da Dama
Dec 23, 2016 05:50A jiya alhamis jami'an tsaro a kasar Demokradiyyar Congo Sun kame mutane da dama da su ka shiga Zanga-zanga.
-
'Yan Adawa Na Gudanar Da Zanga-Zanga A Birane Daban-Daban Na Kasar Sudan
Dec 19, 2016 10:44Magoya bayan jam'iyyun adawa da kungiyoyin farar hula suna gudanar da zanga-zanga a yau a birane daban-daban na kasar Sudan, domin nuna rashin amincewa da matsanancin halin rayuwa da al'ummar kasar suka shiga, inda suke dora alhakin hakan kan abin da suka kira rashin iya mulki na Albashir.
-
Zanga-Zangar Yin Tir Da Allawadai Da Mulkin Kama Karya A Bahrain
Nov 26, 2016 06:50Al'ummar kasar Bahrain sun gudanar da wata gagarumar gagarumar zanga-zanga yin Allawadai da salon mulkin kama karya na masautar Al khalifah a kan al'ummar kasar.
-
'Yan Sanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-Zangar Jin Jinin Shugaban Guinea Bissau
Nov 06, 2016 17:36'Yan sanda a kasar Guinea Bissau sun yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga-zangar kin jinin shugaban kasar da kuma kiran da a sake gudanar da zabe a daidai lokacin da kasashen yankin suke ta kokari wajen ganin an kawo karshen rikicin da ya kunno kai a kasar.
-
Masu Zanga-Zanga Sun Bukaci Shugaban Afirka Ta Kudu Yayi Murabus
Nov 02, 2016 17:16Rahotanni daga kasar Afirka ta Kudu na nuni da cewa dubun dubatan al'ummar kasar ne cikin wata zanga-zanga da suka gudanar suka bukaci shugaban kasar Jacob Zuma da yayi murabus daga mukaminsa.
-
An Bukaci Shugaba Zuma Da Manyan Jami'an Jam'iyyar ANC Da Su Sauka Daga Mukamansu
Sep 05, 2016 16:10Wasu 'yan jam'iyyar ANC mai mulki a kasar Afirka ta kudu sun gudanar da wata zanga-zanga a gaban helkwatar jam'iyyar suna masu kiran shugaban kasar Jacob Zuma da sauran manyan kusoshin jam'iyyar da su yi murabus daga mukamansu sakamakon kayen da jam'iyyar ta sha a zaben da ya gudana.
-
An Bindige Sama Da Masu Zanga-Zanga 90 A Kasar Habasha
Aug 08, 2016 18:17Shaidun gani da ido da kuma majiyoyin 'yan adawa a kasar Habasha (Ethiopia) sun bayyana cewar jami'an tsaron kasar sun bindige sama da mutane 90 a yayin da suke gudanar da zanga-zanga a yankunan Oromiya da Amhara da ke kasar.
-
'Yan Adawa A Chadi Sun Sha Alwashin Gudanar Da Zanga-Zanga Duk Da Hanin Gwamnati
Aug 06, 2016 05:15'Yan adawa a kasar Chadi sun sanar da aniyarsu ta gudanar da gagarumar zanga-zangar kin jinin gwamnatin kasar a yau din nan Asabar da kuma gobe Lahadi duk kuwa da haramta musu hakan da gwamnatin kasar ta yi bisa hujjar cewa hakan yayi kusa da lokacin da ake shirin rantsar da shugaban kasar Idriss Deby a ranar Litinin mai zuwa.
-
Shugaban Sojojin Zimbabwe Yayi Barazanar Sa Kafar Wando Guda Da Masu Zangar Zanga A Kasar
Aug 05, 2016 10:14Babban hafsan hafsoshin kasar Zimbabwe Laftanar Janar Valerio Sibanda ya bayyana cewar sojojinsa za su sanya kafar wando guda da masu tunzura mutane wajen fito da gudanar da zanga-zangar kin jinin gwamnati.