An Bindige Sama Da Masu Zanga-Zanga 90 A Kasar Habasha
https://parstoday.ir/ha/news/world-i9352-an_bindige_sama_da_masu_zanga_zanga_90_a_kasar_habasha
Shaidun gani da ido da kuma majiyoyin 'yan adawa a kasar Habasha (Ethiopia) sun bayyana cewar jami'an tsaron kasar sun bindige sama da mutane 90 a yayin da suke gudanar da zanga-zanga a yankunan Oromiya da Amhara da ke kasar.
(last modified 2018-08-22T11:28:44+00:00 )
Aug 08, 2016 18:17 UTC
  • An Bindige Sama Da Masu Zanga-Zanga 90 A Kasar Habasha

Shaidun gani da ido da kuma majiyoyin 'yan adawa a kasar Habasha (Ethiopia) sun bayyana cewar jami'an tsaron kasar sun bindige sama da mutane 90 a yayin da suke gudanar da zanga-zanga a yankunan Oromiya da Amhara da ke kasar.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar  lamarin ya faru ne lokacin da masu zanga-zangar wadanda suka fito dauke da kwalaye suna rera taken Allah wadai da gwamnatin kasar da kuma bukatar da a sako jami'an 'yan adawa da gwamnatin ta ke rike da su suka yi taho mu gama da jami'an tsaron a kokarinsu na tarwatsa masu zanga-zangar.

Rahotannin sun ce cikin watannin da suka gabata dai yankin na Oromiya ya fuskanci rikice-rikice sakamakon wasu shiri da gwamnatin ta shigo da shi na sauya wajajen noman mutanen yankin, sai dai kuma lamarin yayi kamari ne bayan da gwamnatin kasar ta ki ta saki 'yan adawan da take rike da su.

'Yan adawan dai sun ce 'yan sandan da sauran jami'an tsaro sun yi ruwan albarusai kan masu zanga-zangar a wadannan garuruwa biyu lamarin da yayi sanadiyyar mutuwar alal akalla mutane 90. Har ya zuwa yanzu dai gwamnatin kasar ba ta ce komai kan wannan zargin ba sai dai jaridun gwamnatin sun ce jami'an tsaro sun sami nasarar kawo karshen zangar da wadanda ta kira masu adawa da zaman lafiya suke yi.