Masu Zanga-Zanga Sun Bukaci Shugaban Afirka Ta Kudu Yayi Murabus
Rahotanni daga kasar Afirka ta Kudu na nuni da cewa dubun dubatan al'ummar kasar ne cikin wata zanga-zanga da suka gudanar suka bukaci shugaban kasar Jacob Zuma da yayi murabus daga mukaminsa.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya bayyana cewar masu zanga-zangar wadanda suka fito daga manyan jam'iyyu da kungiyoyi na 'yan adawar kasar suna bukatar shugaba Zuman ne da yayi murabus daga mukamin nasa saboda zarginsa da gazawa da kuma batun rashawa da cin hanci.
Har ila yau wasu rahotannin sun ce babbar jam'iyyar adawa ta kasar ta Democratic Alliance ma ta gudanar da wani gangami na daban duk dai da nufin cimma wannan manufar.
Zanga-zangar dai tana zuwa ne a lokacin da aka fitar da wani rahoto da aka kira da "State of Capture" wanda tsohon mai shigar da kara a kasar Afirka ta Kudun ya shirya wanda ya zargi shugaba Zuma da wasu ministocinsa da rashawa da cin hanci.
Shugaba Zuman dai yayi kokari wajen ganin ba a fitar da wannan rahoto ba, to sai dai babbar kotun kasar ta ki amincewa da wannan bukata ta shugaban inda aka fitar da rahoton.