-
Yan Majalisar Dokokin Zimbawe 230 Ne Suka Bayyana Aniyarsu Ta Tsige Mugabe A Zaman Majalisar Na Yau
Nov 21, 2017 06:59A yau Talata ce ake saran majalisar dokokin kasar Zimbabwe zata tsige shugaban kasar Robert Mugabe daga kujerar shugabancin kasar, bayan da a jiya Litinin yan majalisa 230 cikin 260 suka amince zasu tube shi.
-
Daliban Jami'ar Zimbabwe Sun Yi Zanga-Zangar Kin Jinin Mugabe
Nov 20, 2017 19:00Daliban jami'ar kasar zimbabwe sun gudanar da zanga-zanga ta neman shugaba Robert Mugabe ya sauka daga kan karagar milki.
-
Mugabe Ya Ki Amincewa Yayi Murabus Daga Shugabanci Duk Kuwa Da Matsin Lamba
Nov 20, 2017 05:58A daren jiya ne shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya gabatar da jawabin da al’ummar kasar suka jima suna jiran jin daga wajensa tun bayan rikicin da ya kunno kai a kasar bayan da sojoji suka kwace madafan iko da kuma yi masa daurin talala, to sai dai kuma sabanin abin da aka zata shugaba Mugabe ya sanar da aniyarsa ta ci gaba da mulki duk matsayar da jam’iyyarsa ta ZANU-PF ta dauka na sauke shi daga shugabancin jam’iyyar da kuma zanga-zangar da al’ummar kasar suka yi na bukatar da ya sauka.
-
Shugaba Mugabe Yana Da Dama Zuwa Gobe Litinin Na Ya Yi Murabus Daga Kujerar Shugabancin Kasar Ko A Tube Shi
Nov 19, 2017 19:00A yau lahadi ne jam'iyyar Zanu-PF mai mulki a kasar Zimbabwe ta tube shugaba Robert Mugabe a matsayin shugaban Jam'iyyar sannan ta maye gurbinsa da mataimakinsa da ya kora a makon da ya gabata. sannan ta bada kada da sa'o'i 24 da ya yi ritaya daga shugabancin kasar ko kuma a tube shi.
-
Zimbabwe : Matasan Zanu PF Sun Bukaci Mugabe Ya Yi Murabus
Nov 19, 2017 09:49Kungiyar matasan jam'iyyar Zanu PF mai mulki a Zimbabwe sun bukaci shugaban kasar Robert Mugabe da ya yi murabus daga mulki, tare kuma da tsige matarsa daga jam'iyyar.
-
Shugaba Zuma: Kasashen Afirka Za Su Goyi Bayan Al'ummar Zimbabwe
Nov 18, 2017 16:25Shugaban kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma ya bayyana cewar gwamnatocin kasashen Afirka za su ci gaba da goyon bayan al'ummar kasar Zimbabwe sakamakon rikicin siyasa da ya kunno kai a kasar bayan da sojoji suka kwace madafun iko a kasar da kuma ci gaba da yi wa shugaban kasar Robert Mugabe daurin talala.
-
Dubban Mutane Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Bukatar Mugabe Ya Sauka Daga Mulkin Zimbabwe
Nov 18, 2017 16:23Rahotanni daga kasar Zimbabwe sun bayyana cewar dubun dubatan mutane ne suka taru a yau din nan Asabar a birnin Harare, babban birnin kasar Zimbabwen don gudanar da wata zanga-zangar kirar Shugaba Robert Mugabe da ya yi murabus daga shugabancin kasar.
-
Zimbabwe : Ana Zanga-zangar Neman Mugabe Ya Yi Murabus
Nov 18, 2017 11:19A Zimbabwe wasu al'ummar kasar sun fara zanga-zangar neman shugaban kasar Robert Mugabe da ya yi murabus daga mulki.
-
Zimbabwe: Jam'iyya Mai Mulki Ta Bukaci Shugaba Mugabe Da Ya Yi Murabus
Nov 18, 2017 06:16Shugabanin jam'iyar Zanu-PF mai mulki a kasar Zimbabwe ta bukaci shugaban kasar Robert Mugabe da ya yi murabus daga kan kan mukaminsa.
-
Zimbabwe : Mugabe Ya Fito Bainar Jama'a
Nov 17, 2017 10:51A Karon farko tun bayan da sojoji suka kwace iko da wasu mahimman wurare a Harare babban birnin kasar Zimbabwe, shugaban kasar Rober Mugabe ya fito fili bainar jama'a.