Pars Today
Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, wanda a halin yanzu yake tsare a gidansa na kansa a birnin Harare ya ki amincewa da yi murabus daga kujerar shugabancin kasar.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bukaci dukkanin bangarorin kasar Zimbabwe da su dauki matakin warware dambaruwar siyasar da ta kunno kai a kasar ta hanyar tattaunawa.
Rahotanni sun bayyana cewar manzannin shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma na musamman sun isa kasar Zimbabwe da nufin kawo karshen rikicin da ya kunno kai a kasar tun bayan da sojojin kasar suka kwace madafun iko kasar don 'kame masu laifi' da suke cikin gwamnatin Mugaben a cewarsu.
Shugaban kungiyar tarayya Afrika a wannan karo, kana shugaban kasar Guinea, Alpha Conde ya yi tir da abinda ya ce yana kama da juyin mulki a kasar Zimbabwe.
Sojojin kasar Zimbabwe sun bada labarin cewa sun sauke shugaban kasar Robert Mugabe daga kan kujerar shugabancin kasar
Rahotanni daga kasar Zimbabwe sun ce an ga motoci masu sulke sun kama hanyar babban birnin kasar Harare.
Rahotanni daga kasar Zimbabwe sun bayyana cewar tsohon mataimakin shugaban kasar Zimbabwe da aka kora a ranar Litinin din da ta gabata Emmerson Mnangagwa ya gudu daga kasar saboda abin da na kusa da shi suka kira barazanar da ake yi wa rayuwarsa.
Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya kori mataimakinsa Emmerson Mnangagwa daga mukamin mataimakin shugaban kasar saboda zargin rashin yi masa biyayya.
Tun bayan da hukumar lafiya ta duniya ta zabi shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe a matsayin jakadan kekywan fata na hukumar a wannan shekara, hukumar take shan suka musamman daga bangaren kungiyoyin kare hakkin bil-adama.
Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya bayyana a jiya Asabar kan cewa nan ba da dadewa ba zai bayyana ra'ayinsa kan wanda zai gaje shi tsakanin matarsa da kuma mataimakinsa kan kujerar shugabancin kasar.