An Sauke Shugaba Robert Mugabe Daga Shugabancin Kasar
Sojojin kasar Zimbabwe sun bada labarin cewa sun sauke shugaban kasar Robert Mugabe daga kan kujerar shugabancin kasar
Kamfanin dillancin Labaran reuter ya nakalto majiyar sojojin tana fadar haka a kafafen yada labarai na kasar kan cewa a halin yanzu shugaban dan shekara 97 da iyalansa suna tsare a cikin gidansa, Sannan sojojin zasu gurfanar da wasu sojojin da suke kusa da tsohon shugaban kasar wadanda suke da hannu wajen lalata tattalin arzikin kasar da kuma lalata lamura da dama a cikin kasar.
Amma Emmerson Mnangagwa mataimakin Mugebe da ya sauke a kwanakin baya kuma dan jam'iyyar ZANU-PF mai mulki ya ce babu wani juyin mulki sai dai za'a sauya shugabancin kasar cikin ruwan sanyi.
Babbar jam'iyyar adawa ta kasar Zimbabwe ta yi maraba da matakin da sojojin suka dauka, kuma ta ce tana fatan za'a dawo kan tsarin democradia na gaskiya bayan haka.