Sojoji Sun Kame Muhimman Wurare A Kasar Zimbabwe
(last modified Wed, 15 Nov 2017 06:32:19 GMT )
Nov 15, 2017 06:32 UTC
  • Sojoji Sun Kame Muhimman Wurare A Kasar Zimbabwe

Rahotanni daga kasar Zimbabwe sun ce an ga motoci masu sulke sun kama hanyar babban birnin kasar Harare.

Jaridar independent ta ambato shedun ganin ido suna cewa; Motocin soja masu sulke sun rufe dukkanin hanyoyin da suke shiga cikin babban birnin kasar Harare, yayin da tankokin yaki suka tsaya a gefen titin da ke shiga cikin babban birnin kasar.

A daren jiya ne babban hafsan hafsoshin sojan kasar Janar Kansatanatino Shivinga ya yi barazar cewa Idan har shugaban Mugabe bai janye sauke mataimakinsa ba, to sojojin kasar za su tsoma bakinsu.

Babban hafsan hafsoshin kasar ya ce sauya mataimakin shugaban kasar zai haddasa rashin zaman lafiya a cikin kasar.

A cikin kwanakin nan ne dai shugaba Robert Mugabe ya sauke mataimakinsa Emmerson Mnangagwa. daga kan mukaminsa wanda yake da karfin iko da kuma karbuwa a tsakanin sojojin kasar.

'Yan adawa sun zargi Mugabe da share fagen nada matarsa a kan mukamin na mataimakin shugaban kasa da kuma maye gurbinsa a shugabancin kasar anan gaba.

Wasu rahotannin sun ce kakakin sojan kasar  Maj Gen SB Moyo da ya yi jawabi ta kafafen watsa labarun kasar ya ce; Shugaba Mugabe da iyalansa suna cikin koshin lafiya, kuma sun zo ne domin  su yi maganin masu laifi da ke zagaye da shugaba Mugabe, da suke haddasa matsalar tattalin arziki a kasar.