Tsohon Mataimakin Shugaban Zimbabwe Da Aka Kora Ya Gudu Daga Kasar
(last modified Thu, 09 Nov 2017 11:22:16 GMT )
Nov 09, 2017 11:22 UTC
  • Tsohon Mataimakin Shugaban Zimbabwe Da Aka Kora Ya Gudu Daga Kasar

Rahotanni daga kasar Zimbabwe sun bayyana cewar tsohon mataimakin shugaban kasar Zimbabwe da aka kora a ranar Litinin din da ta gabata Emmerson Mnangagwa ya gudu daga kasar saboda abin da na kusa da shi suka kira barazanar da ake yi wa rayuwarsa.

Kafafen watsa labarai sun jiyo wasu majiyoyin na kurkusa da shi suna fadin cewa tsohon mataimakin shugaban kasar ya tsere daga kasar ne sakamakon barazanar da rayuwarsa take fuskanta tun bayan da aka kore shi daga mukamin mataimakin shugaban kasar, sai dai kuma ba a fadi takamammen inda ya ke ba.

Har ila yau a wata sanarwa da aka jingina ta ga tsohon mataimakin shugaban kasar Zimbabwen ya ce a nan gaba zai dawo kasar don jagorantar al'ummar Zimbabwe yana mai zargin shugaba Mugabe da matarsa Grace da juya jam'iyyarsu ta Zanu-PF mai mulki.

A ranar litinin din da ta gabata ce dai shugaba Mugabe dan shekaru 93 a duniya, ta bakin ministan watsa labaran kasar ya sanar da korar mataimakin shugaban kasar Emmerson Mnangagwa wanda ya zarga da rashin yi masa biyayya da kuma yin zagon kasa. A jiya Laraba kuma jam'iyyar Zanu-PF din ta kori Mr. Mnangagwa din daga jam'iyyar.