Ana Saran Shugaban Zimbabwe Zai Bayyana Magajinsa Da Kansa Nan Gaba
(last modified Sun, 10 Sep 2017 14:48:10 GMT )
Sep 10, 2017 14:48 UTC
  • Ana Saran Shugaban Zimbabwe Zai Bayyana Magajinsa Da Kansa Nan Gaba

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya bayyana a jiya Asabar kan cewa nan ba da dadewa ba zai bayyana ra'ayinsa kan wanda zai gaje shi tsakanin matarsa da kuma mataimakinsa kan kujerar shugabancin kasar.

Muryar JMI ta nakalto Mugabe wanda shi ne shugaban kasa mafi tsufa a duniya yana fadar haka, ya kuma kara da cewa ko da ya bayyana ra'ayinsa ga daya daga cikin mutanen biyu, jam'iyyarsa ta ZANU-PF ce take da magana ta karshe. A halin yanzu dai Mugabe dan shekara 93 a duniya  shi ne dan takarar shugaban kasa na Jam'iyyarsa ta ZANU-PF a zaben shekara ta 2018 mai zuwa. 

Mugabe ne ya jagorancin samarwa kasar 'yancin kai a shekara 1980 kuma tun lokacin yake iko da kasar.  Emmerson Mnangagwa mataimakin shugaban kasa da kuma Grace Mugabe ne suka nuna sha'warsu na gadar Mugabe a duk lokacin da rai ya yi halinsa ko kuma ya sauka daga kujerar shugabancin kasar.