Shugaba Mugabe Na Zimbabwe Ya Kori Mataimakinsa Saboda "Rashin Biyayya"
(last modified Tue, 07 Nov 2017 11:18:00 GMT )
Nov 07, 2017 11:18 UTC
  • Shugaba Mugabe Na Zimbabwe Ya Kori Mataimakinsa Saboda

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya kori mataimakinsa Emmerson Mnangagwa daga mukamin mataimakin shugaban kasar saboda zargin rashin yi masa biyayya.

Kafafen watsa labarai sun bayyana cewar Ministan yada labarai na kasar Simon Khaya Moyo, ne ya sanar da hakan inda ya ce shugaba Mugaben ya kori mataimakinsa Emmerson Mnangagwa ne saboda rashin biyayyarsa ga shugaba Mugaben, kamar yadda kuma yayi zargin cewa mataimakin shugaban kasar ba ya gudanar da ayyukansa yadda ya kamata.

Tun da jimawa dai an jima ana rade-radin korar mataimakin shugaban kasar saboda alamun kai ruwa rana da ke gudana tsakanin mutanen biyu sakamakon karin samun magoya baya da yake yi a tsakanin 'ya'yan jam'iyyar Zanu PF mai mulkin kasar.

Haka dai yana nuni da irin ci gaba da rikicin siyasa da ake fama da shi ne a kasar Zimbabwen.