Zimbabwe : Matasan Zanu PF Sun Bukaci Mugabe Ya Yi Murabus
Kungiyar matasan jam'iyyar Zanu PF mai mulki a Zimbabwe sun bukaci shugaban kasar Robert Mugabe da ya yi murabus daga mulki, tare kuma da tsige matarsa daga jam'iyyar.
A sanarwar da ta fitar yau Lahadi, kungiyar matasan ta Zanu PF, ta ce tana bukatar a tsige Grace Mugabe daga jam'iyyar ba tare da wata wata ba, kana shi ma Mugabe ya yi Murabu daga mukamin shugaban kasa da kuma na shugaba kana sakataren jam'iyyar.
Wannan kiran na zuwa ne kwana guda bayan zanga-zangar da milyoyin 'yan kasar suka gudanar a jiya na neman shugaban kasar ya yi murabus daga mulki.
A wani labari kuma a yau ne ake sa ran shugaban kasar mai shekaru 93 zai gana da sojojin kasar dake tsare da shi tun bayan da suka kwace iko da wasu mahimman wurare a Harare babban birnin kasar.