Pars Today
Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa kisan daruruwan fararen hula a rikicin kabilancin dake faruwa a kasar Demokaradiyar Congo na a matsayin cin zarafin bil-adama.
Bangarorin tarayyar tarayyar Afrika da kuma gwamnatin Iran sun tattauna kan batun bunkasa harkokin ilimi da bincike a tsakaninsu.
Majalisar dokokin kasar Habasha ta ayyana zaman makoki na kwana guda yau Litini, domin juyayin mutane 157 da suka rasa rayukansu a hatsarin jirgin saman fasinja na kamfanin Ethiopian Airlines.
Yau Lahadi, al'umma a Guinea Bissau na kada kuri'a a zaben 'yan majalisar dokokin kasar, wanda ake fatan zai kawo karshen rikicin siyasar da kasar ke fama dashi.
Ma'aikatar tsaro a Nijar ta sanar da mutuwar sojojinta bakwai a wani hari da mayakan boko haram suka kai a kudu maso gabshin kasar.
Fadar shugaban kasar Gabon ta yi watsi da jita-jitan da ke yawo cewa an yi wa wani mutum na daban gyaran kamanni domin ya ci gaba da mulkin kasar a madadin shugaban kasar Ali Bango da ke fama da rashin lafiya.
A Najeriya, yau ne al'ummar kasar ke kada kuri'a a zaben 'yan zaben gwamnoni da 'yan majalisun jihohi.
A Sudan jama'ar kasar da dama ne suka fito yau Alhamis domin gudanar da wata zanga zanga ta kalubalantarkafa dokar ta bacin da shugaban kasar Omar Al' Bashir ya kafa.
Gwamnatin Nijar, ta sanar da dage haramcin kamun kifi, da noman tattasai da kuma kasuwancinsa a jihar Diffa.
A Yau ne kasar Ghana take bikin cika shrekaru 62 da samun ‘yancin kai daga mulkin mallakar Birtaniya