Bunkasa Harkokin Ilimi Da Bincike Tsakanin Iran Da Tarayyar Afrika
(last modified Mon, 11 Mar 2019 15:06:52 GMT )
Mar 11, 2019 15:06 UTC
  • Bunkasa Harkokin Ilimi Da Bincike Tsakanin Iran Da Tarayyar Afrika

Bangarorin tarayyar tarayyar Afrika da kuma gwamnatin Iran sun tattauna kan batun bunkasa harkokin ilimi da bincike a tsakaninsu.

Kamfanin dillancin labaran IRNA ya bayar da rahoton cewa, a  yau an gudanar da tattaunawa tsakanin wata babbar tawaga ta kungiyar tarayyar Afrika karkashin jagorancin babbar kwamishiniya kan harkokin ilimi da bicnike ta kungiyar tarayyar Afrika Sarah Agbor, da kuma jami'ai a ma'aikatun ilimi da bincike da kuma harkokin tattalin raziki na kasar Iran.

da farko tawagar ta fara ganawa ne da mataimakin ministan bukasa harkokin ilimin kimiyya da fasaha na kasar ta Iran a birnin Tehran, inda suka tattauna kan muhimman batutuwa da bangarorin biyu za su gudanar da ayyuka domin amfanin al'ummominsu.

Daga bisani kuma a yau mataimakin ministan harkokin tattalin arziki na kasar Iran ya gana da tawagar ta kungiyar tarayyar Afrika, inda suka cimma matsaya kan muhimman batutuwa da bangarorin biyu za su yi aiki tare musamamn harkokin cinikayya da saka hannayen jari da sauran bangarorin da bangarorin biyu za su ci moriyar juna.