-
Nijar : Hama Amadu Ya Rasa Mukaminsa Na Dan Majalisa
Jun 21, 2018 01:24Jagoran 'yan adawa na Nijar, kana shugaban jam'iyyar Moden Lumana, Hama Amadu, ya rasa mukaminsa na dan majalisar dokoki.
-
Libiya : An Kori Kwamanda, Bisa Zargin Safara Bil Adama
Jun 21, 2018 01:23Rundinar sojin ruwan Libiya, ta sanar da korar kwamandan sojin gabar ruwan lardin Zawyiya, wanda kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya, ya kakaba wa takunkumi bisa zarginsa da safarar bil adama.
-
Kamaru : An Ware Dala Milyan 22 Don Agaza Wa Jama'a A Yankin Dake Fama Da Rikici
Jun 21, 2018 01:23Gwamnatin Jamhuriya Kamaru, ta ware kudade da yawansu ya kai Bilyan 12,7 na CFA, kwatancin Dalar Amurka, Miliyan 22,7, domin agaza wa jama'a a yankin masu magana da harshen Ingilishi dake fama da rikici a kasar.
-
Gwamnatin Kongo Ta Ce Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar Da Kotun ICC Ta Sake Yana Iya Dawowa Gida
Jun 19, 2018 01:19Gwamnatin kasar Demokradiyyar Kongo ta sanar da cewa tsohon mataimakin shugaban kasar, Jean-Pierre Bemba, da kotun duniya mai shari'ar manyan laifuffuka (ICC) ta wanke na iya komawa gida, sai dai ba ta ce ko za a hukunta shi a kasar idan ya dawo ba.
-
Habasha Da Somalia Sun Bukaci A Yaki Ta'addanci
Jun 17, 2018 13:05Shugabannin kasashen Somaliya da Habasha sun bukaci hadin gwiwar kasa da kasa domin yakar ayyukan ta'addanci a doron duniya.
-
Najeriya : 'Yan Kunar Bakin Wake Sun Kashe Mutum 31 A Borno
Jun 17, 2018 11:46Rahotanni daga Najeriya na cewa akalla mutane 31 ne suka rasa rayukansu a wasu jerin hare-haren kunar bakin wake biyu da ake danganta wa dana kungiyar Boko Haram a shiyar arewa maso gabashin kasar.
-
Majalisar Kasar Kongo Na Shirin Kafa Dokar Ba Da Kariya Ga Tsoffin Shugabannin Kasar
Jun 17, 2018 01:21Majalisar kasar Demokradiyyar Kongo ta sanar da cewa nan gaba kadan za ta gudanar da wani zama na musamman don tattauna bukatar da shugaban kasar Josepj Kabila ya gabatar mata na kafa wata doka da za ta ba wa tsoffin shugabannin kasar wata kariya ta musamman.
-
'Yan Takara 23 Zasu Fafata A Zaben Zimbabwe
Jun 14, 2018 22:36A Zimbabwe 'yan takara 23 ne suka yi rejista a takara zaben neman shugabancin kasar na ranar 30 ga watan Yuli dake tafe, ciki har da shugaban kasar mai ci Emmerson Mnangagwa.
-
Shugaban E/Guinea Yayi Kira Ga Hadin Kan Kasa Bayan Kokarin Juyin Mulki
Jun 13, 2018 00:57Shugaban kasar Equatorial Guinea, Teodoro Obiang Nguema, yayi kira zuwa da tattaunawa ta kasa don tabbatar da hadin kan kasar don kawo karshen rikici na siyasa da kasar ta shiga ciki tun bayan da shugaban yayi zargin an yi kokarin kifar da gwamnatinsa da kuma dirar mikiyan da jami'an tsaro suka ci gaba da yi wa 'yan adawa.
-
Kasashen Nigeriya Da Maroko Sun Nuna Damuwa Kan Matsalar Ta'addanci A Nahiyar Afrika
Jun 12, 2018 07:52Kasashen Nigeriya da Maroko sun bayyana damuwarsu kan yadda matsalar ayyukan ta'addanci take ci gaba da habaka a nahiyar Afrika.