Libiya : An Kori Kwamanda, Bisa Zargin Safara Bil Adama
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31900-libiya_an_kori_kwamanda_bisa_zargin_safara_bil_adama
Rundinar sojin ruwan Libiya, ta sanar da korar kwamandan sojin gabar ruwan lardin Zawyiya, wanda kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya, ya kakaba wa takunkumi bisa zarginsa da safarar bil adama.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Jun 21, 2018 05:53 UTC
  • Libiya : An Kori Kwamanda, Bisa Zargin Safara Bil Adama

Rundinar sojin ruwan Libiya, ta sanar da korar kwamandan sojin gabar ruwan lardin Zawyiya, wanda kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya, ya kakaba wa takunkumi bisa zarginsa da safarar bil adama.

Jami'in da aka kora shi ne ke jagorantar rundinar gabar ruwan lardin Zawyiya dake nisan kilomita 45 daga yammacin Tripoli babban birnin kasar ta Libiya.

Wata sanarwa da rundinar sojin ruwan Libiyar ta fitar, ta ce matakin ya biyo bayan da mai shigar da kara na gwamnatin Libiya ta fitar kan  sammacin kame jami'in, Abdurrahmane Milad, inda ita kuma rundinar sojin ruwan ta kuma dakatar da aikinsa.

Sanarwar ta kuma ce ana tsare da jami'in har sai lokacin da aka riga aka gama bincike kan zargin da ake yi masa, ciki har dana muzguna wa bakin haure.

A farkon watan Yuni nan ne, kwamitin tsaron MDD, ya sanya wasu jerin takunkumai, da suka hada da toshe kaddarori da hana fita kasashen waje da kuma sammacin kasa da kasa, kan wasu mutane shida da ake zargi da hannu a safarar bil adama a kasar ta Libiya.