Nijar : Hama Amadu Ya Rasa Mukaminsa Na Dan Majalisa
(last modified Thu, 21 Jun 2018 05:54:08 GMT )
Jun 21, 2018 05:54 UTC
  • Nijar : Hama Amadu Ya Rasa Mukaminsa Na Dan Majalisa

Jagoran 'yan adawa na Nijar, kana shugaban jam'iyyar Moden Lumana, Hama Amadu, ya rasa mukaminsa na dan majalisar dokoki.

Kotun tsarin mulkin kasar ce ta sanar da hukuncin a jiya Laraba.

Tuni kuma aka maye gurbin, Hama Amadu wanda tsohon kakakin majalisar dokokin kasar ne da mataimakinsa Hima Garba.

Hama Amadu, wanda ke gudun hijira a Faransa, an yanke masa hukuncin daurin shekara guda ne bisa zargin safara jarirai daga makobciyar kasar Najeriya, zargin da Hama Amadun da jam'iyarsa ke ci gaba da musuntawa suna masu danganta wa da bita da kulin siyasa kawai.