-
Ma'aikatar Tsaron Rasha: An Fara Aiwatar Da Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Siriya
Feb 27, 2016 12:25Ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar da cewa an fara aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta a yankuna 48 na lardunan Halab, Homs da kuma Damaskus, babbar birnin kasar Siriya kamar yadda aka cimma a baya.
-
Sakataren Harkokin wajen Amurka Ya Bukaci Majalisar Kasar Ta Dakatar Da shirin Tsawaita wasu takunkumai a kan Iran
Feb 26, 2016 01:43Sakatarin harkokin wajen kasar Amurka John Kerry Ya bukaci Majalisar dokokin kasar ta jinkirta tsawaita wasu jerin takunkuman da aka dorawa JMI wadanda kuma zasu kawo karshe a wannan shekara.
-
Shugaban Rasha Ya Tattauna Da Shugaban Siriya Kan Rikicin Kasar
Feb 24, 2016 07:38A wata tattaunawa ta wayar tarho da suka yi a tsakaninsu, shugabannin kasashen Rasha da Siriya sun yi musayen ra'ayi a tsakaninsu kan yadda za a magance rikicn da ya ki ci ya ki cinyewa a kasar Siriyan.
-
Amurka Ta Bukaci Turkiyya Ta Daina Kai Hari Kan Dakarun Kurdawa Da Sojojin Siriya
Feb 14, 2016 09:03Wannan dai ya biyo bayan samun wasu bayanan cewa Turkiyya na kai hare-hare kan dakarun a arewacin Siriya.
-
Amurka : Trump Da Sanders Sun Lashe Zaben Fidda Gwani
Feb 10, 2016 08:26Hakan ya tabbatar da jagorancin Trump a takarar Jam’iyar Republican yayin da Bernie Sanders ya bada mamaki wajen kayar da Hillary Clinton.
-
Gwamnatin Saudiyya Da Batun Tura Sojojinta Zuwa Kasar Siriya
Feb 08, 2016 02:08Har ya zuwa yanzu ana ci gaba da samun mabambanta ra'ayuyyuka dangane da sanarwar da gwamnatin Saudiyya ta yi na shirin da take da shi na tura sojojinta zuwa kasar Siriya, lamarin da gwamnatin Amurka ta yi maraba da shi a daidai lokacin da wasu a Turai kuma suke ci gaba da nuna dari-darin su kan hakan.
-
Kamfanin Twitter Ya Rufe Shafinsa Ga Mutane Sama Da Dubu 125
Feb 06, 2016 08:20Sama Da Mutane dunbu 125 ne kamfanin sadarwar nan na Twitter ya rufewa shafinsa sanadiyar alakarsu da kungiyoyin 'yan ta'adda
-
Matambayi: Dalilan Da Ya Sanya Shugabannin Amurka Mika Kai Ga Sahyoniyawa
Feb 02, 2016 11:53Yanzu kuma bari mu je ga tambayar mu ta biyu a cikin wannan shirin wacce ta fito daga mai saurarenmu Malam Sirajo Ammani daga Yola jihar Adamawan Nigeria wanda yake cewa don Allah ku yi min karin bayani dangane da dalilin da ya sanya shugabannin Amurka musamman 'yan mazan jiyan da suka kafa gwamnati a kasar a baya-bayan nan suke mika kai ga yahudawa dari bisa dari.
-
Jagora Ya Ba Da Lambar Girma Ga Kwamandojin Da Suka Kame Sojojin Ruwan Amurka A Iran
Jan 31, 2016 11:59Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ba wa kwamandojin sojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran su biyar da suka jagorancin kame sojojin ruwan Amurka da suka shigo ruwan kasar Iran a kwanakin baya lambar girma ta "fath' (nasara) don jinjinawa wannan namijin kokari da suka yi na kare kasarsu.